Ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan da takwaransa na Iran, Abbas Araghchi, sun yi magana ta wayar tarho game da tattaunawar nukiliyar da za a yi a Istanbul ranar Juma’a.
Yayin tattaunawar wayar ta ranar Litinin, sun yi nazari kan yanayin rashin jinƙai da ake ciki a Gaza da kuma ababuwan da ke faruwa a Syria, in ji majiyoyin diflomasiyyar Turkiyya.
Za a yi wani sabon zagaye na tattauanawa kan nukiliya tsakanin Iran da ƙasashen Turai uku da aka fi sani da E3, Birtaniya da Faransa da Jamus, a birnin Istanbul na Turkiyya, ranar Juma’a.
Daga farko, Tehran ta ce za karɓi baƙuncin jami’an Rasha da China ranar talata domin tattauna shirinta na nukiliya.
“Muna neman shawarar waɗannan ƙasashen biyu a ko da yaushe domin hana ƙaƙaba takunkumi “snapback” ko kuma rage raɗaɗinsa,” kamar yadda mai magana da yawun bakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Esmaeil Baghaei ya shaida wa manema labarai a Tehran, wanda kamfanin dillancin labaran Tasnim da gwamnatin ƙasar ke da iko a kai.
Yiwuwar ƙaƙaba takunkumin “snapback” a ƙarƙshin yarjejeniyar nukiliya ta shekarar 2015 ta bai wa ƙasashen da suka rabbata hannu a kanta damar iya sake ƙaƙaba takunkumin Mjalisar Ɗinkin Duniya a kan Iran idan aka same ta da laifin rashin mutunta yarjejeniyar.
“Ba mu da shirin tattaunawa da Amurka a ciki yanayin da ake a yanzu,” in ji Baghaei. An kasance ana tattaunawa tsakanin Tehran da Amurka ta hanyar masu shiga tsakani na ƙasar Oman har zuwa lokacin da isr’aila ta kai harin bazata kan Iran ranar 13 ga watan Yuni, lamarin da ya haddasa yaƙin na kwanani 12.
Harin ya zo ne kwanaki biyu kafin kafin a yi zagane na shida na tattaunawa a babban birnin ƙasar Oman Omani, Muscat.
Iran ta zargi Amurka da hannu a harin Isra’ila, da ya kashe manyan jami’an sojin Iran da masana kimiyar nukiliya da kuma fararen hula. Amurka ta kuma ƙaddamar da hare-hare kan manyan tashoshin nukiliyar Iran uku, inda ta yi iƙirarin cewa ta shafe su. Yarjejeniyar tsagaita wuta dai ya kama aiki raar 24 ga watan Yuni.














