Majalisar ƙwararru ta Iran mai mambobi 88 ta zaɓi Mojtaba Khamenei a matsayin sabon jagoran addinin ƙasar bayan kisan da aka yi wa mahaifinsa, Ali Khamenei, a hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai. Malamin mai shekaru 56 ya zama jagoran addini na uku tun bayan juyin juya halin Iran na 1979, kuma ya hau kan mulki a lokacin da yankin Gabas ta Tsakiya ke fuskantar tashin hankali mai tsanani.
An haifi Mojtaba a shekarar 1969 a birnin Mashhad, kuma ya yi karatun addini a Qom, cibiyar manyan makarantun addinin Iran. Duk da cewa bai taɓa tsayawa takarar wani muƙamin siyasa ba, ana ganin ya dade yana da tasiri a cikin da’irar shugabancin ƙasar, musamman saboda kusancinsa da tsohon jagoran addinin da kuma alaƙarsa da Rundunar Kare Juyin Juya Halin Iran (IRGC).
Mojtaba ya fi shahara da aiki a bayan fage, kuma ba kasafai ake ganinsa yana yin jawabai ko shiga muhawarar siyasa a bainar jama’a ba. Duk da haka, sau da dama sunansa kan fito a tattaunawar siyasa, musamman idan ana maganar zaben shugaban kasa ko shugabannin da ke da tasiri a ƙasar.
Naɗinsa na zuwa ne a lokacin da Iran ke cikin wani yanayi mai cike da tashin hankali da barazana daga waje. Isra’ila ta riga ta yi barazanar cewa duk wanda zai gaji Ali Khamenei zai iya zama makasudin hari, lamarin da ke nuna irin matsin lamba da sabon jagoran zai fuskanta yayin da yake karɓar ragamar jagoranci.














