CBN ya ƙaddamar da jakadun kare martabar naira a ƙasar

Cardoso ya ce kuɗin da bankin ke kashewa wajen samar da takardun kuɗin tsaftattu masu ɗorewa zai iya samun tasirin da ake so ne kawai idan mutanen ƙasa suka yi amfani da kuɗin yadda ya kamata bayan an fara aiki da ita.
24 Jun, 2026
‘Yanta’adda sun kashe manoman 11 a arewa maso gabashin Nijeriya

‘Yanta’addan sun tattara manoma bakwai a ranar Asabar a ƙauyen Kuwawu da ke jihar Borno sannan suka yi musu yankar rago, kamar yadda ‘yan bijilanti na yankin suka shaida.
21 Jun, 2026
Gwamna Biodun Oyebanji na jam’iyyar APC ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Ekiti a karo na biyu

Sakamakon ya nuna cewa gwamnan ya samu nasarar ne a karo na biyu da kuri’u 319,224, inda ya doke sauran abokar takararsa na jam’iyyun PDP da ADC da suke bin bayansa.
21 Jun, 2026
Ana gudanar da zaɓen gwamna a Jihar Ekiti da ke kudancin Nijeriya

Yayin da gwamna mai ci, Biodun Oyebanji, ke neman wa’adi na biyu, ana kallon zaɓen a matsayin wani gwaji na ƙarfin jam’iyyun siyasar ƙasar gabanin babban zaɓen Nijeriya mai zuwa.
20 Jun, 2026

Rashin hukunta masu laifi na ƙara haifar da zarge-zargen kisan kare-dangi a Nijeriya: MDD

Tsoffin janar-janar a Nijeriya sun nemi a yi wa harkar tsaro garambawul bayan rasuwar Rabe Abubakar

Sojojin Nijeriya sun ceto mutum hudu da aka sace daga gungun ‘yanta’adda a Katsina

Shugaba Tinubu ya amince a ɗauki jami’an kare daji 1,000 a Jihar Katsina

Kotu ta umarci a dakatar da aiwatar da hukuncin soke rijistar jam’iyyar ADC da wasu jam’iyyu
17 Jun, 2026
Nijeriya ta kama mutane takwas saboda yaɗa labarai marasa tushe
Gwamnatin Nijeriya ta kama aƙalla mutane takwas a ‘yan makonnin nan saboda yaɗa labaran ƙarya a kafofin sada zumunta.

16 Jun, 2026
Bankin Duniya ya ayyana tashoshin jiragen ruwan Apapa da Tincan cikin 20 da suka fi inganci a duniya
A cikin rahotonsa na yanayin aiki da kontena (CPPI) na shekarar 2025, Bankin Duniya ya lissafa tashoshin jiragen ruwa na Tincan Island da na Apapa a cikin tashoshi 20 waɗanda suka sake inganta.

16 Jun, 2026
‘Yanbindiga sun kashe aƙalla mutum 20 Jihar Kebbi ta Nijeriya
Hukumomi sun yi Allah wadai da kashe-kashen kuma sun sha alwashin ɗaukar matakan tsaro yayin da hare-haren ƙungiyoyin ‘yanbindiga ke ƙaruwa.

15 Jun, 2026
Gwamnatin Nijeriya ta gurfanar da fiye da mutum 400 a kotu a Abuja kan zarginsu da ta’addanci
Ana gurfanar da wadanda ake zargin cikin rukuni-rukuni a dakunan kotun daban-daban inda aka dakatar da shari’o’i da dama don ba wa alkalai damar sauraron shari’ar, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

15 Jun, 2026
Kotun Nijeriya ta ba INEC umarnin soke rajistar ADC da wasu jam’iyyu huɗu
Mai Shari’a Peter Lifu, a cikin wani hukunci da ya yanke, ya umarci hukumar INEC da ta soke rajistar wasu jam’iyyun siyasa saboda sun kasa samun kashi 25 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa a babban zaɓen da ya gabata, kamar yadda doka ta tanada.

15 Jun, 2026
Dakarun Nijeriya sun ƙaddamar da farmaki kan ’yanta’adda a Katsina bayan kashe tsohon Janar na soja
Tun bayan fara aikin, dakarun sun gudanar da sintiri na yaƙi, hare-haren da aka tsara bisa bayanan sirri, ayyukan kewaye da bincike, da kuma farmakin share maboyar masu laifi a wurare daban-daban da aka gano a yankin ayyukan rundunar.

14 Jun, 2026
Erdogan ya jinjina wa Turkiyya kan komawa Gasar Kofin Duniya bayan shekara 24
Shugaban Turkiyya ya bayyana cewa ‘yan ƙasar na cikin farin ciki tare da goyon bayan ‘yan wasan, ya kuma tuna da tarihin da ƙasar ta kafa na samun matsayi na uku a Gasar Kofin Duniya ta 2002, inda ya ce lokaci ya yi da za a rubuta sabon tarihi tare.

14 Jun, 2026
Boko Haram ta ƙona wasu makarantun firamare da sakandare a Jihar Borno
Lamarin na zuwa ne bayan an sace ɗaliban makarantar Firamare da Sakandare ta Mussa da ke Askira-Uba kusan wata guda da ya gabata, ba tare da an gano inda suke ba.

13 Jun, 2026
Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya ya rasu a hannun ‘yanbindiga
Gwmnatin Jihar Katsina ce ta tabbatar da rasuwar tsohon janar ɗin a wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar inda ta ce ya rasu ne sakamakon matsalolin rashin lafiya da suka shafi ciwon sukari da hawan jini yayin da yake tsare a hannun ‘yanbindiga.

13 Jun, 2026
‘Yanbindiga sun kashe manoma 17 a Jihar Zamfarar Nijeriya
Kungiyoyin ‘yan bindiga da suka ƙware wajen satar mutane domin neman kudin fansa da kuma satar shanu suna addabar al’ummomi a arewaci da tsakiyar Nijeriya, inda suke kai hare-hare masu muni tare da ƙaƙaba haraji ga manoman da ke son zuwa gonakinsu.



