INEC za ta rufe rijistar masu zaɓe ranar Lahadi, ‘yan adawa na neman a tsawaita lokacin rijistar

A wani saƙon da ta wallafa a shafinta na X ranar Lahadi, hukumar ta ce za a rufe rijistar ranar Lahadi 26 ga watan Yuli inda ta ce mutane za su iya ƙarƙare rijistarsu ta intanet cikin sa’o’in da suka saura.
26 Jul, 2026
Sojojin Nijeriya sun ce suna ƙoƙarin ceto shugaban ƙaramar hukumar Bungudu a Zamfara

Bayanai sun nuna cewa ‘yanbindiga sun sace shugaban ƙaramar hukumar Bungudu, Nura Umar Abdullahi da iyalansa bayan sun kashe jami’an tsaronsa a harin da suka kai gidansa da sanyin safiyar ranar Asabar.
25 Jul, 2026
Dangote na shirin samar da wurin ajiyar mai a Kamaru

Labarai da dumi-duminsu, ra’ayoyi, maƙalu, sharhi, da hotuna daga TRT Afrika, a ko yaushe
25 Jul, 2026
An yi jana’izar manoma 26 da aka kashe a harin ‘yanbindiga a Jihar Zamfara a Nijeriya

Hukumomin yankin sun ce an kai wa manoman harin ne yayin da suke aiki a gonakinsu a Ƙaramar Hukumar Kaura Namoda ta Jihar Zamfara a ranar Alhamis.
24 Jul, 2026

Rundunar Sojin Nijeriya na neman jami’inta ruwa-a-jallo kan zargin sayar wa ‘yanta’adda kayan soji

ICPC ta miƙa filin ginin gidaje 962 na aikin dala miliyan 65 ga Bankin Lamunin Gidaje na Nijeriya

Matatar Dangote ta koma sayar da fetur a naira, ta ƙara farashin lita da N140

Trump ya yabi Tinubu kan ‘jagorancinsa a yaƙi da ta’addanci’ a Nijeriya

Nijeriya ta kaddamar da shirin takardun lamuni na N729bn don biyan basussuka a fannin lantarki
22 Jul, 2026
An yi garkuwa da fiye da mutum 40 a hare-haren ‘yanbindiga a Jihar Zamfara
A cewar wani mazaunin gundumar Mayanchi da ke ƙaramar hukumar Maru, maharan sun kai hare-hare a ƙauyuka 11 tsakanin ranar Juma’a da Lahadi, inda suka kai farmaki al’ummomin Tashar Mayanchi, Gwargawo, Jidda da Garagi, da sauransu.

21 Jul, 2026
NESREA ta fara bincike kan zargin zubewar sinadari a babbar hanyar Kaduna-Abuja
Tawaga daga ofishin NESREA reshen Jihar Kaduna, ƙarƙashin jagorancin Kodinetan jihar, Hena Dangari Emmanuel, ta kai ziyara wurin domin tantance abin da ya faru tare da fara bincike.

21 Jul, 2026
Jami’an tsaron Nijeriya sun kama ɗanta’adda ɗan ƙasar Sudan da wata mace ‘yar Ghana a Borno
Dakarun da ke kai farmakan HADIN KAI sun kama wani dan kasar Sudan da ake zargi da zama dan ta’adda daga kasar waje, tare da wata mace ‘yan kasar Ghana a yankin Askira/Uba da ke jihar Bornon Nijeriya.

21 Jul, 2026
DSS ta Nijeriya za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin ɗaurin rai da rai da aka yanke wa shugabannin Ansaru
Hukumar DSS ta Nijeriya ta soki hukuncin da aka yanke wa shugabannin Ansaru inda ta ce hukuncin bai dace da girman laifukan da suka aikata ba.

20 Jul, 2026
Ana fargabar mutane 40 sun mutu sakamakon kifewar kwale-kwale a jihar Jigawa a ke Nijeriya
Ana ci gaba da ayyukan bincike da ceto a Jihar Jigawa ta Njeriya bana kwale-kwale dauke da mata da yara ‘yan firamare ya kife a Karamar hukumar Ringim, inda ake fargabar rasa rayuka akalla 40.

19 Jul, 2026
An kashe ɗalibai yayin da sojoji suka ‘ceto ɗalibai 46’ daga harin satan ɗalibai a Borno
Babu tabbacin ko ɗalibai da suka rasun ‘yan makarantar FGGC Monguno ne ko kuma ‘yan Kolejin Kimiyya da Fasahar.

18 Jul, 2026
Dakarun Nijeriya sun kuɓutar da mutum 12 da aka yi garkuwa da su a jihohin Katsina da Benue
Kazalika sojojin sun samu sun ƙwato shanu 56 tare da kashe wasu daga cikin waɗanda ake zargi da kasancewa cikin masu garkuwa da mutanen.

17 Jul, 2026
Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da shirye-shiryen ayyukan Bankin Duniya na dala biliyan 3.05
An shirya ayyukan ne da zummar tabbatar da cewa alkhairin sauye-sauyen sun kai ga mutane ta hanyar inganta rayuwa da kuma damar samun muhimman hidindimu.

17 Jul, 2026
Fiye da mutum 1,000 ne suka tsere wa hare-haren ‘yanbindiga a jihar Benue ta Nijeriya
Maharan sun afka wa al’ummar Ankpechi da ke gundumar Oglewu ta karamar hukumar Ohimini a safiyar Alhamis, inda suka tilasta wa mazauna yankin barin gidajensu su nemi mafaka a al’ummomin da ke makwabtaka, a cewar jami’an yankin.

17 Jul, 2026
Kotun Nijeriya ta ba da umarnin ƙwace kadarorin Aisha Achimugu na kusan Naira biliyan 9
Kadarorin da aka ƙwace sun haɗa da kayan ado da darajarsu ta kai Naira biliyan 4.645, motoci 11 na alfarma da darajarsu ta kai Naira biliyan 4.293, da kuma dala 50,000 da Naira miliyan 30 lakadan.



