Pakistan ta sanar da mutuwar sojojinta 12 da jikkatar wasu 27 sakamakon arangama da sojojin Afghanistan a kan iyaka. Kakakin rundunar, Laftanar Janar Ahmed Sharif Chaudhry, ya ce ana kuma neman wani soja guda da ya ɓace.
A cewarsa, rundunar saman Pakistan ta kai hare-hare a Kabul, Kandahar da Paktia, inda ya yi iƙirarin cewa an kashe daruruwan mayaƙa tare da lalata wuraren ajiyar makamai da sansanonin soji. Ya jaddada cewa ba a kai hari kan fararen hula ba, yana mai cewa Pakistan ta ɗauki matakin ne don kare kanta.
Sai dai ma’aikatar tsaron Afghanistan ta ce akalla sojojinta takwas sun mutu, tare da zargin cewa sojojin Pakistan 55 ne suka rasa rayukansu. Ba a iya tabbatar da adadin asarar da bangarorin ke ikirari ba saboda ci gaba da faɗa.
Rikicin ya ƙara tsananta bayan Kabul ta ce ta mayar da martani kan hare-haren da Pakistan ta kai a ciki ƙasar. A halin yanzu, Pakistan ta haramta duk wani amfani da jiragen sama marasa matuƙi a faɗin ƙasar saboda matsalar tsaro.













