Nijeriya

Ranar Hausa ta Duniya: Harshen Hausa ya gawurta, in ji Shugaba Tinubu

“Hausawa manyan turaku ne da ke taka muhimmiyar rawa wajen tsayuwar Nijeriya da cigabanta,” in ji Tinubu.

Newstimehub

Newstimehub

26 Aug, 2026

77ac56d5 f4f1 4737 8b44 937e0d28bb80 1780344752851

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya taya Hausawa murnar zagayowar Ranar Hausa ta Duniya, inda ya bayyana al’ummar Hausawa a matsayin muhimman ginshiƙai na haɗin kai da ci gaban Nijeriya.

A saƙon da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta ranar Laraba, Shugaba Tinubu ya ce harshen Hausa ya gawurta, kuma ‘‘ya zama babban harshen haɗin kai da tattalin arziki a duniya baki ɗaya.”

Hausawa manyan turaku ne da ke taka muhimmiyar rawa wajen tsayuwar Nijeriya da cigabanta,” in ji Tinubu.

Shugaban ya kuma yi nuni kan yadda harshen ke ci gaba da yaɗuwa, yana mai cewa ya haɓaka sosai a tsawon shekaru kuma yana matsayin babban harshe na haɗin kai da kasuwanci a wajen iyakokin Nijeriya.

A cewarsa, yawan amfani da harshen Hausa yana nuna muhimmancin harsunan asali wajen haɓaka hanyoyin sadarwa da fahimtar al’adu da haɗin kan tattalin arziki tsakanin al’ummomi.

Bikin wanda ke gudana a Fadar Masarautar Daura mai tarihi a Jihar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Nijeriya, na nuna muhimmacin tushen tarihin Hausawa da kuma gadon gargajiya waɗanda suka ba da gudunmawa ga asalin Nijeriya.

Miliyoyin mutane ne suke magana da harshen Hausa a Arewacin Nijeriya da Jamhuriyar Nijar da Kamaru da Chadi da kuma wasu ƙasashe a Yammaci da Tsakiyar Afirka, abin da ya sanya harshen ya zama na farko da ake amfani da shi a Afirka.

Kazalika saƙon na Tinubu ya jaddada muhimmancin bambancin al’adu a Nijeriya, inda al’ummar Hausawa ke zama muhimmin ɓangare na tushen haɗa al’adu daban-daban na ƙasar.