Ma’aikatar Baitulmalin Amurka ta sanar da cewa za a sanya sa hannun Donald Trump a kan sabbin takardun kuɗin ƙasar, a wani ɓangare na bikin cika shekaru 250 da kafuwar Amurka. Hukumomin sun ce wannan shi ne karo na farko a tarihi da sa hannun shugaban ƙasa mai ci zai bayyana a kan irin waɗannan takardun kuɗi.
A cewar bayanin da aka fitar, sa hannun Trump zai kasance tare da na Sakataren Baitulmali a kan sabbin takardun da za a buga. An bayyana hakan a matsayin wani mataki na musamman da aka ɗauka domin nuna muhimmancin wannan babban biki na ƙasa.
Sakataren Baitulmali Scott Bessent ya ce a ƙarƙashin jagorancin Trump, Amurka na tafiya zuwa ga bunƙasar tattalin arziki da ba a taɓa gani ba, ƙarfin dala mai ɗorewa, da kuma daidaiton harkokin kuɗi. Ya ƙara da cewa sanya sa hannun Trump a kan dala wata hanya ce ta girmama abin da ya kira nasarorin tarihi na ƙasar da kuma na shugaban ƙasar a daidai lokacin bikin shekara 250.














