Matatar Mai ta Dangote ta bukaci ‘yan Najeriya da su rika kai rahoto kan duk wani gidan mai na MRS da ke sayar da fetur (PMS) sama da farashin da aka amince da shi na ₦739 kowace lita. Matatar ta bayyana cewa ta fara sayar da fetur a fadin ƙasar nan a wannan farashi ta dukkanin gidajen mai na MRS Oil Nigeria Plc.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi, kamfanin ya ce rage farashin fetur din wata babbar nasara ce a kokarinsa na samar da mai mai araha ga ‘yan Najeriya tare da daidaita kasuwar man fetur a kasa. Dangote ta bayyana cewa, kasancewar MRS na da sama da gidajen mai 2,000 a fadin Najeriya, ana sa ran aiwatar da wannan sabon farashi a dukkan rassa domin amfanin ya kai ga jama’a baki daya.
Matatar ta yaba wa ‘yan kasuwa da suka rungumi sabon tsarin farashin, tare da kira ga sauran masu gidajen mai da su yi koyi da su domin taimakawa farfadowar tattalin arzikin kasa. Kamfanin ya kuma jaddada cewa yana da tabbacin samar da lita miliyan 50 na fetur a kullum, lamarin da zai sauya yanayin samar da mai musamman a wannan lokacin bukukuwa. Ta hanyar tace mai a cikin gida, matatar na rage dogaro da kasuwannin waje, kare kudin kasar waje, da kuma karfafa tsaron makamashi a Najeriya.
Sai dai Dangote ta gargadi wasu ‘yan kasuwa marasa gaskiya da ka iya kirkirar karancin mai domin kawo cikas ga rage farashin, tana mai kira ga hukumomin gwamnati da su dauki matakin gaggawa kan irin wadannan dabi’u. Matatar ta kuma shawarci ‘yan Najeriya da kada su sayi fetur a farashi mai tsada yayin da ake samun mai mai inganci a ₦739 daga gidajen MRS. Ta bukaci jama’a da su kai rahoton duk wani gidan MRS da ke sayar da fetur sama da wannan farashi ta lambar waya 0800 123 5264.
A karshe, matatar ta sake jaddada kudirinta na samar da wadataccen mai, daidaita farashi, da tabbatar da tsaron makamashi, tana mai cewa burinta shi ne amfanin dogon lokaci ga kasa baki daya, ba ribar gajeren lokaci ba.














