Ƙungiyar Tarayyar Afirka da Kungiyar Ƙasashen Larabawa sun yi Allah-wadai da matakin Isra’ila na amincewa da Somaliland a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta, suna masu cewa hakan na barazana ga haɗin kai da zaman lafiyar yankin Kahon Afirka.
Tarayyar Afirka (AU) ta bayyana cewa ba za ta amince da duk wani yunƙuri na ɗaukar Somaliland a matsayin ƙasa mai ‘yanci ba, tana mai sake jaddada matsayinta na kare haɗin kan Somalia, ikon ƙasarta da kuma cikakken yankunanta.
A wata sanarwa da AU ta fitar ranar Juma’a, shugaban hukumar ƙungiyar, Mahmoud Ali Youssouf, ya ce babu shakka Somaliland har yanzu wani ɓangare ne na Jamhuriyar Tarayyar Somalia, kuma duk wani mataki da zai karya wannan tsari na iya kafa mummunan tarihi ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a Afirka.
Kungiyar ta ce irin waɗannan matakai sun saɓa wa muhimman ka’idojin Tarayyar Afirka, musamman girmama iyakokin da aka gada tun lokacin samun ‘yancin kai.
A gefe guda kuma, Kungiyar Ƙasashen Larabawa ta yi kakkausar suka kan matakin Isra’ila, inda Sakataren Janar ɗinta, Ahmed Aboul Gheit, ya bayyana shi a matsayin mataki mai tayar da hankali da barazana ga tsaron yankin.
Ya ce amincewar ta saɓa dokokin ƙasa da ƙasa da ƙa’idojin ikon ƙasa da kiyaye iyaka da ke kunshe cikin Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya, yana mai jaddada cewa Somaliland na nan a matsayin cikakken ɓangare na Somalia da duniya ta amince da ita.
Kungiyar ta kuma yi kira ga al’ummar duniya da su yi watsi da duk wani mataki da zai iya ƙara rikitar da harkokin tsaro a yankin Kahon Afirka.
Somaliland ta ayyana ‘yancin kanta tun 1991, amma har yanzu ba ta samu amincewa daga Majalisar Dinkin Duniya ko Tarayyar Afirka ba, yayin da gwamnatin Somalia ke ci gaba da kallonta a matsayin ɓangare na ƙasar.
Majiyar Labari: TRT WORLD














