Nijeriya

Sarki Charles ya amince da ‘mummunan’ mulkin mallakar da Birtaniya ta yi wa Nijeriya

Sarkin Birtaniya ya amince da akwai “lokuta a tarihin kasashen biyu [Birtaniya da Nijeriya] wadanda na sani sun bar mummunan tabon” yayin jawabin da ya yi a wajen kasaitacciyar liyafar cin abinci.

Newstimehub

Newstimehub

19 Mar, 2026

7f415f3222568dbf64888cc38d8dfc0626fbb3658488cb0cce2b4f759fe5033d

Sarki Charles na III a ranar Laraba ya yaba da “huldar cude-ni-in-cude-ka” tsakanin Birtaniya da Nijeriya yayin da ya karbi bakuncin Shugaba Bola Tinubu a ziyarar aiki ta farko da shugaban kasar da ta fi kowace yawan jama’a a Afirka ya kai cikin kusan shekaru arba’in.

Amma yayin da yake magana kan tarihin Nijeriya a matsayin kasa wacce Birtaniya ta yi wa mulkin mallaka, Sarki Charles ya amince da cewa akwai “lokuta a tarihin kasashen biyu [Birtaniya da Nijeriya] wadanda na sani sun bar mummunan tabon” yana mai cewa “babu wasu kalamai” da za su iya kawar da shi.

Liyafar, wadda aka gudanar a fadar Windsor Castle mai tarihi wadda ke yammacin Landan, ta samu halarcin Sarki Charles da Sarauniya Camilla inda suka karbi bakuncin Tinubu da matarsa, tare da jami’an gwamnatin Nijeriya, masana harkokin banki, ’yan kasuwa, taurarin wasanni, da kuma shahararrun mutane ’yan asalin Nijeriya.

“Birtaniya da Nijeriya suna da ‘dankon zumunci mai karfi’ da kuma ‘kawaye da ke cin moriyar juna wanda ya kawo mana manyan fa’idoji baki daya,’” in ji sarkin yayin da yake jawabin bude taron.

Shugaba Tinubu ya shaida wa sarkin cewa “kasashenmu biyu suna da fata kan makoma irin daya don ci gaba” bisa ga “mutunta juna da alkibla daya,” yana mai bayyana cewa shi ne shugaban Nijeriya na farko da ya taba yin jawabi a fadar Windsor Castle.

Charles ya kwatanta Nijeriya a matsayin “katafariyar kasa ta fuskar tattalin arziki,” inda ya ce kasar “ba wai kawai ta sauya ba ne, ta riga ta kai matakin ci gaba.”

Cikin mutanen da suka halarci liyafar har da ministoci da manyan mutane kamar shugaban bankin Moniepoint, Tosin Eniolorunda.

Kazalika akwai kyaftin din kungiyar Rugby ta Ingila Maro Itoje, zakarar Olympics Christine Ohuruogo, tsohuwar ’yar wasan kwallon kafa Eniola Aluko da marubuci Ben Okri, da kuma fitacciyar mawakiya Tiwa Savage.

Sarki Charles ya yi amfani da kalmomin Yarabanci da na “Pidgin” a cikin jawabin nasa, wanda hakan ya sa Shugaba Tinubu dariya da yin tafi.

Shugaban Nijeriyar ya mayar da martani ga gaisuwar da sarkin ya yi masa da yaren Yarbanci ta hanyar yin dariya da tafi.

Shugaba Tinubu Musulmi ne, kuma Sarki Charles ya gode masa bisa yin ziyararsa da kawo masa a lokacin watan Ramadan, wanda ya ce “ba karamin sadaukarwa ba ne,” sannan ya yi masa “Barka da Azumin Ramadan” Wannan ita ce walima ta farko da aka taba yi wa shugaban kasa Musulmi a lokacin Ramadan tun shekarar 1928, inda aka samar da dakin sallah da kuma buda baki kafin cin abincin dare.

A ranar Alhamis, ana sa ran Shugaba Tinubu zai gana da Firaiministan Birtaniya Keir Starmer, wanda shi ma ya halarci walimar. Kuma ana saran shugaban zai gana da ’yan Nijeriya mazauna Birtaniya.

Ziyarar aiki ta karshe da shugaban Nijeriya ya kai Birtaniya ya yi ne a shekarar 1989, ko da yake Sarki Charles ya taba  karbar bakuncin Tinubu a watan Satumban 2024.

Kafin rasuwar mahaifiyarsa, Sarauniya Elizabeth II, a shekarar 2022, Charles ya ziyarci Nijeriya har sau hudu a lokacin yana matsayin Yariman Wales, inda ziyararsa ta karshe ta kasance a shekarar 2018.