Gwamnatin Saudiyya ta sanar da cewa dakarunta sun yi nasarar tare jiragen sama marasa matuki guda biyu da suka yi yunƙurin kai hari kan matatar mai ta Ras Tanura, wadda kamfanin Aramco ke mallaka. Lamarin ya faru ne da safiyar Litinin a gabashin ƙasar, a daidai lokacin da rikicin yankin ke ƙara kamari.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Tsaro, Turki Al-Maliki, ya ce an tarwatsa jiragen kafin su kai ga harin da ake zargi da shiryawa. Sai dai ya bayyana cewa ɓaraguzan jiragen sun faɗi kusa da wuraren fararen hula, lamarin da ya haddasa ƙaramar gobara ba tare da jikkatar kowa ba. Bidiyoyin da suka bazu a kafafen sada zumunta sun nuna hayaƙi yana tashi daga yankin matatar.
Hare-haren na zuwa ne a lokacin da tashin hankali ke ci gaba da ƙaruwa a Gabas ta Tsakiya. A kwanakin baya, Saudiyya ta ce wasu sassan ƙasar, ciki har da Riyadh, sun fuskanci hare-hare daga Iran. Wannan kuma ya biyo bayan farmakin da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, wanda daga baya Iran ta mayar da martani da kai hare-hare a Isra’ila da wasu ƙasashen yankin da ke dauke da sansanonin Amurka.
Rikicin da ke gudana ya ƙara tayar da hankalin kasuwannin makamashi da tsaron yankin, musamman ganin muhimmancin matatar Ras Tanura a harkar samar da mai a duniya.














