Shugaban Somalia, Hassan Sheikh Mohamud, ya bayyana amincewa da sabon kundin tsarin mulkin ƙasar a matsayin wani muhimmin ci gaba a tarihin siyasar Somalia. A wata jawabi ga al’umma, ya ce kammala kundin tsarin mulkin ya kawo ƙarshen tsarin wucin gadi da ƙasar ta yi amfani da shi tsawon shekaru.
Sabon kundin tsarin mulkin ya samu amincewa ne bayan majalisar dokokin ƙasar ta kada kuri’a domin yin wasu manyan sauye-sauye da nufin ƙarfafa shugabanci da samar da tsari mai inganci ga tsaro da tattalin arziki. Shugaban ya ce wannan mataki zai taimaka wajen ƙarfafa cibiyoyin gwamnati da kuma kawar da wasu matsalolin tsarin siyasa da suka dade suna hana cigaba.
Sai dai wasu ‘yan adawa da kuma wasu gwamnatocin yankuna kamar Puntland da Jubaland sun soki matakin, suna cewa sauye-sauyen kundin tsarin mulki ya kamata su kasance da cikakken amincewar dukkan bangarorin siyasa.














