Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya gana da Yarima Mai Jiran Gado na Saudiyya Mohammed bin Salman a Riyadh ranar Talata, a cewar Shugaban Sadarwa na Turkiyya. Ganawar ta gudana ne a wani zama na sirri, ba tare da bayyana cikakkun bayanai kan abin da aka tattauna ba.
A ziyarar aiki zuwa Saudi Arabia, Erdogan ya kasance tare da Uwargidan Shugaban Ƙasa Emine Erdogan da manyan jami’an gwamnati, ciki har da Ministan Harkokin Waje Hakan Fidan, Ministan Kuɗi Mehmet Simsek da Ministan Tsaro Yasar Guler. Bayan ganawar, MBS ya shirya liyafar cin abinci ta musamman domin girmama shugaban Turkiyya a Fadar al-Yamamah.
Ziyarar ta Riyadh ita ce mataki na farko a rangadin Erdogan a yankin. Daga nan, ana sa ran shugaban zai wuce Cairoranar Laraba bisa gayyatar Shugaban Masar Abdel Fattah el-Sisi, domin halartar taron Majalisar Haɗin Kai ta Manyan Matakai tsakanin Turkiyya da Masar.
A yayin ziyarar Alkahira, ana sa ran shugabannin za su tattauna dangantakar ƙasashen biyu da batutuwan yankin da na duniya, tare da mai da hankali kan halin da ake ciki a Falasdinu. Haka kuma, Erdogan na shirin halartar Taron Kasuwanci na Turkiyya da Masar domin ƙarfafa hulɗar tattalin arziki.
Majiyar Labari: TRT HAUSA














