Nijeriya

Sojojin Nijeriya Sun Gano Wurin Boye Man Fetur da Kayayyaki na Boko Haram a Borno

Sojojin Nijeriya sun gano maboyar man fetur da kayayyakin Boko Haram a ƙarƙashin ƙasa a Borno bayan kai samame a sansanoninsu

Newstimehub

Newstimehub

20 Jan, 2026

4beeea36b46e1c3c12a8061eecb8f74ca9baf30f0cef9a53c988f34d0884c4b7

Dakarun Sojin Nijeriya sun sake samun gagarumar nasara a yaƙin da suke yi da ƙungiyoyin ta’addanci a Arewa maso Gabas, bayan gano wasu manyan wuraren ɓoye makamai, magunguna da man fetur na Boko Haram a ƙarƙashin ƙasa a yankin Timbuktu Triangle da ke Jihar Borno, lamarin da ke nuna irin dabarun da ’yan ta’addan ke amfani da su wajen ci gaba da kai hare-hare.

Rundunar Hadin Kai ta Operation Desert Sanity ta kai samame a yankunan Chilaria, Garin Faruk da Abirma bayan samun sahihan bayanan sirri, inda ta lalata sansanonin Boko Haram da ISWAP tare da jawo musu mummunar asara. Jami’in yada labarai Laftanal Kanal Uba Sani ya ce sojojin sama sun bayar da gagarumin tallafi ta hanyar sa ido da bin sahun ’yan ta’adda. A yayin farmakin, an gano harsasai, wayoyi, tutoci, buhun hatsi, magunguna, dizal, da wurin ɓoye man fetur a ƙarƙashin ƙasa da ’yan ta’adda ke amfani da su wajen gudanar da ayyukansu.

 

Majiyar Labar: TRT HAUSA