Rundunar Sojin Najeriya sun kashe mayaƙan Boko Haram 16, bayan arangama da suka yi da su a yankin Komala da ke ƙaramar hukumar Konduga.
Kakakin rundunar, Laftanal Kanal Sani Uba, ya ce farmakin ya biyo bayan yunƙurin harin da ’yan ta’addan suka nemi kaiwa sansanin sojoji a Auno a farkon watan Fabrairu, wanda dakarun suka daƙile. Rundunar ta ce maharan sun yi ja da baya kafin sojoji su kai harin ramuwa, inda suka kashe da dama tare da tilasta wa wasu tserewa da raunuka.
Sanarwar ta kara da cewa dakarun sun ƙwace kekuna sama da 20, makamai da kayayyaki, tare da kama wasu da ake zargi da safarar magunguna ga ISWAP.
Haka kuma, an daƙile yunƙurin garkuwa da mutane a hanyar Buratai zuwa Kamuye, inda aka kuɓutar da mutane biyu aka haɗa su da iyalansu. Rundunar ta jaddada cewa ayyukan kakkabe ’yan ta’adda na ci gaba a Borno da kewaye.
Majiyar Labari: TRT HAUSA














