A ci gaba da ƙoƙarin da sojojin Nijeriya ke yi na kawo ƙarshen ta’addanci a Arewa maso Gabas, dakarun Operation Hadin Kai sun samu babbar nasara bayan sun dakile jerin hare-hare da ’yan ta’adda suka kai a jihohin Borno da Adamawa, inda suka hallaka da dama daga cikinsu tare da kwato muggan makamai, lamarin da ya sake tabbatar da ƙarfinsu da shirin kare rayukan fararen hula.
Sojojin sun fatattaki ’yan ta’adda da suka yi yunƙurin kwace sansanin sintiri a Madagali, Jihar Adamawa, tare da hallaka da dama daga cikinsu ba tare da asara a bangaren sojoji ba. A rana ɗaya, an kuma dakile wani babban hari da aka kai sansanin FOB Azir a Jihar Borno, inda sojoji tare da taimakon jiragen sama suka tilasta wa maharan janyewa, suka kwato makamai masu yawa ciki har da bama-bamai, harsasai da roka, tare da tabbatar da tsaron yankunan.














