Sojojin Rundunar Haɗin Gwiwa ta Nijeriya ƙarƙashin Operation HADIN KAI sun daƙile wani hari da ake zargin mayakan ISWAP ne suka kai kan sansanin sojoji a Goniri da ke Jihar Yobe, inda aka kashe fiye da ’yanta’adda 20.
Harin ya fara ne a daren Litinin zuwa wayewar garin Talata, lokacin da maharan suka yi ƙoƙarin kai farmaki daga ɓangarori da dama domin kewaye sansanin sojojin.
Majiyoyin tsaro sun ce an fara gano motsin maharan ne ta hanyar amfani da na’urorin sa ido yayin da suke tahowa daga ƙauyen Goniri da kuma hanyar Ngamdu junction.
Daga nan sojoji suka mayar da martani da ƙarfi, yayin da aka tura ƙarin dakarun taimako da kuma jiragen yaƙi zuwa yankin.
Jiragen yaƙi na rundunar sama da ke aiki tare da Operation HADIN KAI sun bayar da gaggawa daga sama, wanda ya taimaka wajen tilasta wa ’yanta’addan janyewa bayan sun yi asara mai yawa.
Daga cikin waɗanda aka kashe har da wani babban kwamandan ’yan ta’addan mai suna Abu Yusu.
Bayan daƙile harin, sojojin sun ƙwato makamai da kayayyakin yaƙi da maharan suka bari bayan sun tsere, ciki har da bindigogin masu sarrafa kansu da AK-47, bama-bamai na IED da kuma harsasai iri-iri.
Ayyukan bincike da kawar sauran ‘yanta’adda daga daji da sojoji suka yi daga baya a Timbuktu Triangle, musamman a yankin Gwaigomari, sun kai ga gano ƙarin gawarwakin ’yanta’addan a yayin sintiri da aka gudanar har zuwa safiyar Laraba.
Jami’an sojin sun ce wasu daga cikin sojojin na Nijeriya sun samu raunuka a yayin artabun, amma an garzaya da su asibiti kuma suna samun sauƙi.
Sojoji na ci gaba da riƙe yankin, yayin da ake gudanar da ƙarin bincike domin gano ’yanta’addan da suka tsere zuwa wasu al’ummomin da ke kusa.














