Rahotanni daga Najeriya na cewa shugaban Hukumar Alhazan Nijeriya (NAHCON), Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan, ya ajiye aikinsa yayin da ake shirye-shiryen aikin Hajji na 2026. Kawo yanzu ba a bayyana dalilin murabus ɗin ba, amma mai magana da yawunsa, Ahmed Muazu, ya tabbatar da faruwar lamarin. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya naɗa Sheikh Pakistan a 2024 bayan cire Jalal Arabi, wanda aka fara bincike a kansa kan zarge-zargen da suka shafi kuɗaɗen hajji.
Shugabancin Sheikh Pakistan ya fuskanci ce-ce-ku-ce tun bayan Hajjin 2025, inda aka yi ta zarge-zargen badaƙalar kuɗi — iƙirarin da ya haddasa rikici a cikin hukumar. A Janairun 2026, rahotanni sun ce wasu kwamishinonin NAHCON sun kai ƙorafi ga Shugaba Tinubu, suna zargin gazawar shugabanci. Lamarin ya kai ga shiga tsakani da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, wanda ya kira taron sasanci domin kwantar da rikicin.
Majiyar Labari: TRT HAUSA














