Gabas Ta Tsakiya

“Tallafi na Kan Hanya” – Trump Ya Ƙarfafa Masu Zanga-zanga a Iran

A wani rubutu Trump ya ce: “Na soke dukkan ganawar da zan yi da jami’an Iran har sai an daina kai wa masu zanga-zanga hari. Taimako na kan hanyarsa. MIGA!!!”

Newstimehub

Newstimehub

13 Jan, 2026

2026 01 13t072111z 1 lynxmpem0c0aw rtroptp 3 usa trump world order

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa masu zanga-zanga a Iran kira da su ci gaba da matsin lamba kan hukumominsu, yana mai cewa “taimako na kan hanya” tare da gargaɗin cewa jami’an da ke zaluntar jama’a za su fuskanci hukunci.

A wani saƙo da ya wallafa a kafar Truth Social, Trump ya ce ya soke dukkan tattaunawar da zai yi da jami’an Iran har sai an daina kai wa masu zanga-zanga hari, yana mai amfani da taken “MIGA” domin nuna goyon bayansa.

Fadar White House ta ce Trump na buɗe ƙofar diflomasiyya, amma kuma yana la’akari da amfani da ƙarfi idan aka ci gaba da take hakkin masu zanga-zanga. A gefe guda, hukumomin Iran sun zargi Amurka da Isra’ila da goyon bayan tarzoma.

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun ce fiye da mutane 600 sun mutu, sama da 1,000 sun jikkata, yayin da dubban masu zanga-zanga ke tsare a sassa daban-daban na ƙasar.

Majiyar Labari: TRT HAUSA