Shugaban Amurka Donald Trump ya ce rundunar sojin Amurka ta kai hari mai girma a Tsibirin Kharg na Iran kuma ya yi gargaɗin cewa za a iya kai hari kan wuraren mai na ƙasar idan aka ci gaba da kawo tangarɗar jigilar jiragen ruwa ata Mashigin Hormuz.
“Hukumar Sojan Amurka da ke aiki a Gabas ta Tsakiya da wasu ƙasashen Asiaya ta aiwatar da ɗaya daga cikin manyan hare-haren bam a tarihin Gabas ta Tsakiya kuma ta hallaka duk wani wuri na SOJA a wurin da Iran ke taƙama da shi, Tsibirin Kharg,” kamar yadda Trump ya bayyana a safiyar Asabar a shafinsa na sada zumunta.
“Na zaɓi BA zan lalata wuraren mai a tsibirin ba. Duk da haka, idan Iran, ko wani kuma, ya yi wani abu da zai katse wucewar jiragen ruwa cikin ‘yanci da aminci ta Mashigin Hormuz, zan sake tunani nan take.”
Muhimmin tsibiri
Amurka da Isra’ila sun yi taka-tsantsan game da tsibirin, amma an ruwaito cewa jami’an gwamnatin Trump sun ce ƙwace iko da Tsibirin Kharg na cikin abin da ake la’akari da shi yayin da rikicin Amurka da Isra’ila ke ci gaba a Gabas ta Tsakiya.
Tsibirin, wanda yake kusan kilomita 30 daga gabar Iran, yana tafiyar da kusan kashi 90 cikin 100 na fitar ɗanyen mai na Iran, bisa ga wata sanarwa ta baya-bayan nan daga JP Morgan.
Yankin ya kai kusan ɗaya cikin uku na girman birnin Manhattan na New York, kuma masana sun ce kowane ƙoƙari a kansa zai haifar da sakamako cikin sauri.
Hare-haren Iran na ramuwar gayya sun dakatar da zirga-zirgar jiragen ruwa a Mashigin Hormuz, wanda yawanci kashi ɗaya cikin biyar na ɗanyen mai na duniya da iskar gas na LNG ke bi ta tsibirin, kuma hakan ya shafi wuraren mai a wasu kasashen Gulf.
Trump ya ce rundunar sojin ruwa ta Amurka za ta fara yi wa jiragen ruwa na dakon mai rakiya ta Mashigin Hormuz “nan ba da jimawa ba” don dawo da fitar mai, yayin da yake ƙoƙarin magance hauhawar farashin mai a Amurka.
Kharg ya samu ci gaba sosai a lokacin da Iran ke faɗaɗa harkar man ta a shekarun 1960 da 1970.














