Tsohon shugaban Nijeriya kuma shugaban mulkin soja a baya, Muhammadu Buhari, ya rasu yana da shekaru 82 a birnin London, ƙasar Birtaniya, kamar yadda iyalan marigayin suka tabbatar da rasuwarsa da yammacin Lahadi a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Malam Garba shehu ya fitar.
Buhari ya rasu bayan fama da rashin lafiya, kodayake ba a bayyana ainihin abin da ke damunsa ba.
Sha’anin lafiyarsa ta jima tana janyo tambayoyi musamman a lokacin da yake shugabancin ƙasa daga 2015 zuwa 2023, inda ya yi fama da doguwar jinya a ƙasashen waje.
Buhari, wanda ya kasance babban janar na soji, ya fara hawa mulki ne ta hanyar juyin mulki a watan Disamban 1983, inda ya kifar da gwamnatin farar hula ta Shugaba Shehu Shagari.
Mulkinsa ya shahara da tsauri da kuma yaƙi da rashin ɗa’a. Ya kafa shahararren shirin “Yaƙi da Rashin Da’a”, kafin daga bisani a yi masa juyin mulki a 1985 inda Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya maye gurbinsa.
Bayan komawar Nijeriyar tsarin dimokuraɗiyya a 1999, an yi ta kiraye-kiraye ga Muhammdu Buhari kan ya shiga fagen siyasa, wand a lokacin ake da fatan zai iya magance matsalolin da Nijeriya ke fama da su.
Ya shiga harkokin siyasar a shekarun 2000, inda ya yi takarar shugaban ƙasa sau uku ba tare da nasara ba, kafin daga baya ya samu nasara a 2015. Wannan nasarar tasa ta zama tarihi, domin shi ne shugaban ƙasa na farko da ya doke mai ci a zaɓe a tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya.
Gwamnatinsa ta mayar da hankali sosai wajen yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma ƙoƙarin murkushe ‘yan Boko Haram a Arewa maso Gabas. Masoyansa sun yaba masa da tsayuwar daka wajen kare dukiyar ƙasa, sai dai masu suka sun zarge shi da fifita wasu, da tsaurin ra’ayi, da kuma gazawa wajen farfaɗo da tattalin arziki.
Bayan ya kammala wa’adinsa na biyu a watan Mayun 2023, Buhari ya koma garinsu Daura a Jihar Katsina, inda dama tun kafin ya sauka mulki ya sha nanata cewa Daura zai koma domin aikin gona da kula da dabbobinsa.
Buhari ya bar matarsa Aisha Buhari, da ‘ya’ya da jikoki.
Tuni Shugaba Tinubu ya aika da saƙon ta’aziyya tare da umartar mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya tafi Landan domin tahowa da gawar marigayin.