Wannan sabon ci gaban ya ɗaga hankula a fannin kimiyya da tsaro, domin Ministan Masana’antu da Fasaha na Turkiyya, Mehmet Fatih Kacir, ya tabbatar da cewa an kammala nazarin aikin kuma an fara matakin farko na gina tashar sararin samaniya a Somalia. Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya bayyana shirin a taron manema labarai tare da Shugaban Somalia, Hassan Sheikh Mohamud, a Istanbul.
Tashar za a gina ta ne bisa yarjejeniyar haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu, inda aka nuna cewa yankunan da ke kusa da daidaiton duniya kamar Somalia na da babbar fa’ida wajen ƙaddamar da tauraron ɗan’adam. Ministan ya ce wannan zuba jari zai bai wa Turkiyya damar ƙaddamar da satellites ɗinta kai tsaye, ya ƙarfafa masana’antar cikin gida, ya rage dogaro da wasu ƙasashe, tare da kawo babbar fa’ida ta tattalin arziki ga Somalia.
A cewarsa, tashar za ta ba da damar ƙaddamarwa cikin aminci, sauƙi da inganci saboda kyawawan halayen muhalli na Somalia. Haka kuma, za ta zama ginshiƙi wajen haɓaka harkokin bincike da ci gaban fasahar sararin samaniya, tare da ɗaga matsayin Turkiyya cikin ƙasashen da ke da cikakkiyar tashar ƙaddamar da tauraron ɗan’adam.














