Maroko ta kai ga matakin kusa da daf da na ƙarshe a gasar cin kofin duniya yayin da Kanada ta fice

Wannan shi ne lokaci na biyu a jere da Maroko ke kaiwa matakin kusa da daf da na ƙarshe a gasar cin kofin duniya bayan ta zama tawagar Afirka ta farko da ta fara kaiwa matakin daf da na ƙarshe a shekarar 2022.
5 Jul, 2026
Ronaldo da Ramos sun ci ƙwallo yayin da Portugal ta doke Croatia a Kofin Duniya

Goncalo Ramos ya ciyo wa Portugal ƙwallo ta farko yayin da Cristiano Ronaldo ya ci bugun fenareti a wasan da suka doke tawagar Croatia da ke ƙarƙashin jagorancin Luka Modric.
3 Jul, 2026
Belgium ta cire Senegal daga Gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026

Belgium ta samu gurbi a zagayen ‘yan-16 na gasar Kofin Duniya, bayan ta doke Senegal da ci 3-2 a wasansu na ranar Laraba.
2 Jul, 2026
NASA ta sha alwashin aika ƙwallon ƙafa zuwa Duniyar Wata idan Amurka ta lashe Kofin Duniya

Shugaban NASA, Jared Isaacman ya ba da misali da ɗan samajannati, Alan Shepard, wanda ya tafi da ƙwallayen gwaf zuwa duniyar wata a 1971, yana cewa za su yi irin haka idan Amurka ta lashe Kofin Duniya.
1 Jul, 2026

Norway ta fitar da Ivory Coast daga Gasar Kofin Duniya

Canada ta fitar da Afirka ta Kudu a zagayen ‘yan-32 a Gasar Kofin Duniya

Kun san ƙasashen Afirka tara da suka kai zagayen sili-ɗaya-ƙwale a Gasar Kofin Duniya ta 2026?

FIFA tana cire sunan giya daga Kyautar Gwarzon Wasa da ake bai wa ‘yanwasa Musulmi a Kofin Duniya

Mohamed Salah ya jagoranci Masar a nasararta ta farko a Gasar Kofin Duniya a karawa da New Zealand
19 Jun, 2026
Gasar Kofin Duniya: Mexico ta zama ƙasa ta farko da ta tsallaka matakin sili ɗaya ƙwale
Mexico ta yi amfani da kurakuran da ‘yan bayan Koriya Ta Kudu suka yi wajen kasancewa ƙasar da ta fara tsallakawa matakin sili ɗaya ƙwale a Gasar Cin Kofin Duniya.

12 Jun, 2026
An buɗe Gasar Kofin Duniya ta 2026 inda Mexico ta lallasa Afirka ta Kudu 2-0 a Estadio Azteca
Julian Quinones da Raul Jimenez su ne taurarin Mexico a wasan yayin da Afirka ta Kudu ta gaza jefa ƙwallo ko ɗaya a wasan buɗe Gasar ta Kofin Duniya a birnin Mexico City.

8 Jun, 2026
An jikkata aƙalla mutum tara a harbi a kusa da sansanin Ingila a gasar Kofin Duniya a Amurka: Rahoto
‘Yansanda sun mayar da martani kan harbin bindiga da sanyin safiya a kusa wajen na Birnin Kansas, yayin da ake ci gaba da bincike.

7 Jun, 2026
An hana ‘yan jarida da dama na Iran da Afirka bizar shiga Amurka Gasar Kofin Duniya
Ƙungiyar ‘yan jaridar ta wasanni ta aika wasiƙa a ranar Jumma’a ga Bryan Swanson, daraktan hulɗa da jama’a na FIFA da kuma Jochen Steinhoff, shugaban hukumar gudanarwar sashen watsa labarai na ƙwallo.

2 Jun, 2026
Ghana ta bayyana sunayen ‘yan wasa 26 da za su buga mata gasar Cin Kofin Duniya
Za a fara gasar Cin Kofin Duniya ne a Amurka, Canada, da Mexico a ranar 11 ga watan Yuni, Ghana zata fafata da Panama a wasanta na farko a rukunin L bayan kwanaki shida da fara gasar. Sauran kasashen da ke cikin rukunin sun hada da Ingila da Croatia.

1 Jun, 2026
Kofin Duniya na 2026: FIFA za ta fito da sabuwar dokar da ake wa lakabi da “A-kori-Arsenal”
Salon riƙe ƙwallo da ake kira da “Set piece”, wato dabarar tsayar da wasa don saita ‘yanwasa a fili yadda za su ciyo ƙwallo, ya zama wata babbar hanyar cin ƙwallo musamman a gasar Firimiya.

31 May, 2026
Paris Saint-Germain ta lashe gasar Champions League bayan ta lallasa Arsenal a bugun fanareti
Bayan an kasa samun wanda ya yi nasara a ƙarin lokacin da aka yi, PSG ta zama ƙungiya ta biyu da ta riƙe kambunta na lashe kofin.

7 May, 2026
Iran ta ce dole Amurka ta ba da biza ga tawagarta ta Kofin Duniya ba tare da la’akari da siyasa ba
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje ya ambata fatan cewa FIFA za ta ɗauki matakan da suke wajaba ‘domin kare mutuncin gasar’.

6 May, 2026
Karawar PSG da Bayern Munich za ta sake kayatarwa
A wasan farko masana ƙwallo sun soki ‘yanwasan baya na duka ƙungiyoyin, ganin yadda suka bari aka zura ƙwallaye har tara a muhimmin wasa irin wannan.

5 May, 2026
Kungiyoyin Gasar Firimiya ta Ingila sun yi asarar dala biliyan 1 na kudin-shiga: Rahoto
Kashe kuɗaɗe don sayo ‘yanwasa ya yi yawan da ba a taɓa gani ba, wanda ya janyo masoya ƙwallo suna fushi kan kuɗin da ke fita waje yayin da ake neman su biya kuɗin tikita da tsada.



