Wasanni

NASA ta sha alwashin aika ƙwallon ƙafa zuwa Duniyar Wata idan Amurka ta lashe Kofin Duniya

Shugaban NASA, Jared Isaacman ya ba da misali da ɗan samajannati, Alan Shepard, wanda ya tafi da ƙwallayen gwaf zuwa duniyar wata a 1971, yana cewa za su yi irin haka idan Amurka ta lashe Kofin Duniya.

Newstimehub

Newstimehub

1 Jul, 2026

switzerland world cup 2026 playoff soccer draw 20028

Shugaban hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka, NASA ya yi ƙoƙarin ƙarfafa gwiwar ‘yanwasan Amurka a gasar Kofin Duniya ta wannan shekara, yana mai cewa zai aika ƙwallon ƙafa zuwa duniyar wata idan suka lashe gasar.

“Wannan ƙalubale ne, kun gane, Team USA, ku kammala aikinku,” in ji shugaban NASA, Jared Isaacman a ranar Talata yayin wani taron da ya bayyana shirye-shiryen hukumar NASA na gina sansanin a kan wata.

NASA ta riga ta aika ƙwallon FIFA zuwa Tashar Sararin Samaniya ta Duniya (ISS), yayin da Amurka ke zama masaukin baƙi na gasar tare da Mexico da Canada a gasar FIFA 2026.

Amma idan tawagar Amurka ta yi nasara, abin da ba a sa ran faruwarsa sosai, to Isaacman ya yi alƙawarin tura ƙwallon ƙafa zuwa wata duniyar daban.

Ya nuna cewa a 1971, ɗan-sama-jannatin Amurka, Alan Shepard ya shahara kan cewa ya ɗauku wasu ƙwallayen gwaf zuwa wata, bayan ya ɓoye sanda da wasu ƙwallaye.

“Za mu zarce Alan Shepard,” Isaacman ya yi alƙawari yana mai ƙarawa da cewa, “Za mu kai ƙwallon ƙafar nan. Don haka, wannan ba ƙaramar ƙarfafawa ga Amurka ba ce.”