Kimiyya Da Fasaha

WhatsApp ya rufe shafuka fiye da miliyan 6.8 masu alaƙa da zamba: Meta

Kamfanin Meta ya yi kira ga masu amfani su dinga taka tsantsan a duk lokacin da wani da ba su sani ba ya tuntuɓe su – musamman wadanda suka buƙaci a ba su kuɗi ko wasu bayanai da suka shafi mutum.

Newstimehub

Newstimehub

6 Aug, 2025

1754468144761 uur1gv 2c0ddead461b081197d8d7a2171ff6e56b82eeb626a10e4f3f3db3e80988d1e3

WhatsApp ya dakatar da shafuka fiye da miliyan 6.8 da aka danganta da ayyukan damfara a farkon rabin wannan shekarar, in ji kamfanin Meta, mamallakin shafin.

“A matsayin wani bangare na aikinmu na ci gaba don kare mutane daga damfara, WhatsApp ya gano kuma ya dakatar da fiye da shafuka miliyan 6.8 da aka danganta da cibiyoyin damfara,” in ji kamfanin a cikin wata sanarwa a ranar Talata.

Meta ya bayyana cewa an dauki matakin dakatar da shafukan ne kafin a fara amfani da da yawa daga cikinsu, yana mai gode wa bincike mai zurfi da aka yi da kuma ƙarfafa matakan tsaro.