Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa yaƙin da ake yi da ƙungiyar ta’addanci ta Daesh yana ƙara ƙarfi da karsashi, yana mai cewa ana ci gaba da tumɓuke tushen ta’addanci daga yankin Gabas ta Tsakiya. Ya ce kawar da barazanar ‘yan ta’adda musamman a arewacin Syria zai kawo sauƙi ba ga ‘yan Syria kaɗai ba, har da dukkan ƙasashen yankin.
Erdogan ya faɗi hakan ne a yayin bikin miƙa sabbin gidaje a lardin Aydin na Turkiyya, inda ya jaddada muhimmancin haɗin kai wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Syria. A cewarsa, zaman lafiyar Syria zai amfani kowane bangare na al’umma, ciki har da Larabawa, Turkmaniyawa, Kurdawa, Alawiyawa, Druze da Kiristoci.
Shugaban ya kuma ce tattaunawar da aka yi a taron World Economic Forum na Davos ta nuna cewa ƙasashen yammacin duniya na ƙara fahimtar matsayin Turkiyya na sukar tsarin duniya na yanzu, tare da amincewa da bukatar samar da sabon tsari na adalci da tsaro.














