Rahotanni sun nuna cewa ana ci gaba da mummunan artabu a yankin kudancin tsakiyar Sudan tsakanin rundunar sojin gwamnati da dakarun RSF. Sojojin ƙasar sun bayyana cewa sun karɓe gari Mabsouta da ke kudancin Kordofan, sai dai dakarun da ke Arewacin Kordofan na fuskantar hare-haren jiragen sama marasa matuka daga RSF.
Mazauna El-Obeid, babban birnin yankin, sun ruwaito ganin hayaki yana tashi daga wani sansanin soja da ke cikin birnin, alamar tsananin fafatawar. Duk kokarin tabbatar da tsagaita wuta ya gaza, domin bangarorin biyu na dagewa kan wasu sharuɗɗan da ba su dace ko yiwuwa a cika su ba.
Yankunan jihohin Kordofan uku sun kasance tamkar filin yaƙi tun bayan barkewar rikicin siyasa a Sudan sama da watanni talatin da suka gabata, inda RSF ta mamaye yawancin yankin Darfur yanzu haka.














