Wannan mummunan lamari ya girgiza al’ummar Gombe, domin ‘yan jarida bakwai membobin NUJ sun rasu a hatsarin mota yayin dawowa daga ɗaurin auren abokin aikinsu a Kaltungo. Hatsarin ya faru ne bayan tayar motar bas ɗin da suke ciki ta fashe a kan hanyarsu ta komawa gida a kusa da garin Kumo, inda motar ta ƙwace ta nufi cikin daji.
Kwamandan FRSC a Gombe, Samsan Kaura, tare da Daraktan Yaɗa Labarai na Gwamnatin Jihar, Ismaila Misilli, sun tabbatar da mutuwar mutane bakwai da jikkatar wasu huɗu da ke samun kulawa a asibiti.
Waɗanda suka mutu sun haɗa da:
Zarah Umar, Babbar Mataimakiya ta Musamman ga Matar Gwamna
Manu Haruna Kwami, NTA
Musa Tabro, tsohon Manajan Labarai
Aminu Adamu, Direba
Adams Danladi, StarTimes
Judith Kutus, Hukumar SUBEB
Gwamna Inuwa Yahaya ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamatan, yana mai bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga jihar da fagen yada labarai. Ya yi addu’ar rahma ga mamatan da kuma waraka cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.














