Nijeriya

‘Yanbindiga a Nijeriya sun kashe jami’an tsaro da ‘yan bijilanti 20 a Filato

‘Yanbindigar sun kashe jami’an tsaro 12, ciki har da manyan jami’an soja biyu, da kuma ‘yan bijilanti takwas da ke taimaka wa jami’an tsaron wajen kare al’ummomin yankin da abin ya shafa.

Newstimehub

Newstimehub

15 Mar, 2026

4ed0c826d36279e553bf7d41197216d52b9df9a90446faebfc5d451db373a674

Aƙalla jami’an tsaro da ‘yan bijilanti 20 ne aka ruwaito sun mutu bayan da wasu ‘yanbindiga masu ɗauke da manyan makamai suka kai wa tawagar sintiri ta haɗaka harin kwanton-ɓauna a Wanka da wasu al’ummomi da ke yankin Garga a Ƙaramar Hukumar Kanam ta Jihar Filato.

Kungiyar Kanam Development Association (KADA) ce ta sanar da wannan harin ta a cikin wata sanarwa da sakatarenta, ND Shehu Kanam, da shugabanta, Garba G. Aliyu, suka sanya wa hannu, wadda aka fitar ranar Asabar a garin Dengi, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Kanam.

Ƙungiyar ta ce waɗanda suka mutu sun haɗa da jami’an tsaro 12, ciki har da manyan jami’an soja biyu, da kuma ‘yan bijilanti takwas da ke taimaka wa jami’an tsaron wajen kare al’ummomin yankin.

A cewar sanarwar, tawagar sintirin—wadda ta kunshi sojoji da ‘yan bijilanti na yankin—na tafiya ne cikin motoci biyu domin gudanar da sintirin tsaro na yau da kullum a ƙauyukan Garga, Kyaram da Gyambau, lokacin da ɗaruruwan ‘yanbindiga ɗauke da makamai suka yi musu kwanton-ɓauna a hanyarsu ta zuwa Wanka da misalin karfe 2:00 na rana ranar Juma’a.

 “A wannan mummunar musayar wutar wadda ta biyo bayan harin kwanton- ɓaunar, kasar nan ta yi asarar jarumai masu kare ta, waɗanda suka sadaukar da rayukansu a bakin aikinsu.”

Kungiyar ta kara da cewa bayan harin, an ruwaito cewa ‘yanbindigar sun kutsa cikin al’ummar Kyaram inda suka wawushe dukiyoyi na miliyoyin naira tare da kwashe shanu masu yawa na mazauna yankin.

Kungiyar ta kuma ce tun a baya ta sha yin kira ga hukumomi kan tabarbarewar tsaro a yankin, amma ta koka cewa matsalar na ci gaba da tsananta.

Saboda haka ta yi kira ga gwamnatocin karamar hukuma, ta jiha da kuma ta tarayya da su gaggauta ɗaukar matakai domin daƙile karin zubar da jini a al’ummomin da abin ya shafa.