Daruruwan masu zanga-zanga sun taru a birnin Stockholm domin nuna adawarsu ga hare-haren Isra’ila a Gaza da kuma tsoma bakin sojan Amurka a Venezuela, inda suka bayyana damuwa kan abin da suka kira take hakkin bil’adama da karya dokokin kasa da kasa.
Masu zanga-zangar, da suka hallara a filin Odenplan bisa kiran kungiyoyin farar hula, sun ce Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare a Gaza duk da tsagaita wutar da aka cimma a ranar 10 ga Oktoba 2025. Haka kuma sun yi Allah-wadai da tsare shugaban Venezuela Nicolas Maduro da matarsa Cilia Flores da Amurka ta yi.
Sun rika ɗauke da kwalaye masu rubuce-rubuce irin su “Ana kashe yara a Gaza”, “A dakatar da yunwa a Falasdinu”, da “A’a ga yaƙi a Venezuela, eh ga zaman lafiya”, suna kira da a dakatar da hare-haren Isra’ila tare da sakin Maduro da matarsa.
Wata ‘yar gwagwarmaya ‘yar Sweden mai suna Sigrun Meder ta ce suna Allah-wadai da hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Gaza da kuma abin da ta kira sace shugaban Venezuela. Ta jaddada cewa duk da ikirarin tsagaita wuta, har yanzu ana ci gaba da kashe fararen hula a Gaza.
Meder ta kuma ce duniya na cikin wani lokaci da ba a mutunta dokokin kasa da kasa, tana mai cewa ana amfani da doka ne kawai kan wasu kasashe, yayin da manyan kasashe ke kauce mata.














