Ajanda

Ƴan majalisar dokokin Kano biyu sun rasu a rana guda

Ƴan majalisar dokokin jihar Kano guda biyu sun rasu a kusan lokaci ɗaya sakamakon rashin lafiya, kamar yadda gwamnatin jihar ta tabbatar.

Newstimehub

Newstimehub

24 Dec, 2025

079d05d8 0aba 4327 8969 3e9f91c76434.jpg e1766607581501

Jihar Kano ta shiga jimami bayan rasuwar ƴan majalisar dokoki guda biyu a kusan lokaci ɗaya, lamarin da ya girgiza al’umma da kuma majalisar dokokin jihar.

Mai magana da yawun gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya tabbatar da rasuwar a wata sanarwa da ya wallafa a shafukan sada zumunta.

Ƴan majalisar da suka rasu su ne Sarki Aliyu Daneji, mai wakiltar Kano Municipal, da kuma Aminu Sa’ad Ungoggo, wakilin mazaɓar Ungoggo. Rahotanni sun nuna cewa Sarki Aliyu Daneji ya rasu ne kimanin awa ɗaya bayan rasuwar Aminu Sa’ad Ungoggo, kuma dukkaninsu sun mutu sakamakon rashin lafiya.

Majiyar Labari: BBC Hausa