Daruruwan mutane sun yi zanga-zanga a babban birnin Guinea-Bissau a ranar Juma’a, inda suke adawa da juyin mulkin sojoji da aka yi a watan da ya gabata kuma suna neman a saki shugabannin jam’iyyar adawa, yayin da shugabannin yankin ke shirin haduwa a ranar Lahadi don tattauna rikicin.
Masu zanga-zangar sun yi arangama da jami’an tsaro a Bissau, inda suka ƙona tayoyi kuma suka roƙi a saki Domingos Simoes Pereira, Shugaban Jam’iyyar Afirka don ‘Yancin Guinea-Bissau da Cabo Verde (PAIGC), wanda aka kama a lokacin juyin mulkin, a cewar ‘yan uwansa da majiyoyin tsaro.
Jami’an soji sun kori Shugaba Umaro Sissoco Embalo a ranar 26 ga Nuwamba, rana guda kafin hukumar zaɓe ta sanar da sakamakon zaɓen majalisar dokoki da na shugaban ƙasa. Sai washe-gari Rundunar Soji ta nada Manjo Janar Horta Inta-a a matsayin shugaban riƙon ƙwarya.
Shugabannin kungiyar yankin ECOWAS za su yi taro a Abuja, Nijeriya, don tattaunawa kan Guinea-Bissau da yiwuwar sanya takunkumi kan wannan ƙasar ta Yammacin Afirka, in ji Ministan Harkokin Wajen Saliyo, Timothy Musa Kabba, a makon da ya gabata.
“Ba mu amince da gwamnatin wucin-gadi ba,” in ji mai fafutukar al’umma Vigario Luis Balanta a wani taron manema labarai a ranar Jumma’a, yana kiran a yi yajin aiki baki ɗaya da kuma rashin biyya ga gwamnati na mako guda.”
Ba a samu damar tuntubar gwamnatin sojin wucin-gadi nan take don samun sharhi ba.
A ranar Talata, rundunar soji ta bayyana wani kundin tsarin mulki na wucin-gadi na tsawon wata 12 da ke haramta wa Inta-a da firaministansa shiga zaɓuɓɓuka na gaba, ta sanar da wannan shirin makonni biyu bayan da suka dakatar da kundin tsarin mulki.
“Mu matasa ne kuma mu ne makomar wannan ƙasa,” in ji ɗaya daga masu zanga-zangar, Antonio Sami. “Ba za mu taɓa amincewa da kalubalantar ‘yancin kasarmu ba.”
Juyin mulkin ya kasance na tara a Yammaci da Tsakiyar Afirka cikin shekaru biyar, kuma wani ɓangare ne na jerin rashin kwanciyar hankali a Guinea-Bissau. Ƙasar ta shahara wajen zama mashigar safarar hodar ibilis kuma tana da dogon tarihin juyin mulki.














