Turkiyya ta miƙa saƙon ta’aziyyarta ga ƙasar Pakistan ranar Asabar sakamakon mutuwar ɗaruruwan ‘yan ƙasar a ambaliyar ruwa a faɗin ƙasar.
“Muna matuƙar baƙin ciki game da rasa rayukan da aka yi sakamakon ambaliyar ruwa a Pakistan,” a cewar wata sanarwa daga Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya.
Ta ƙara da cewa: “Muna addu’ar Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu kuma muna miƙa ta’aziyyarmu ga Pakistan.”
Hukumomi a Pakistan ranar Asabar sun ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon mamakon ruwan sama da ambaliyar ruwa ya zarta 321.














