Wasanni

Lukaku zai yi jinya har zuwa Nuwamba yayin da Napoli za ta fara kare kambin Serie A bana

Romelu Lukaku na Napoli ya samu rauni a cinya yayin wasan sada-zumunta na share fagen gasar Serie A ta Italiya.

Newstimehub

Newstimehub

18 Aug, 2025

italy soccer 87258

Ɗan wasan Napoli, Romelu Lukaku ya samu rauni a cinyarsa yayin wasan sada-zumunta da Olympiacos, kafin fara gasar Serie A ta Italiya.

Raunin zai tilasta masa tafiya jinyar watanni uku har zuwa Nuwamba, kamar yadda Napoli ta tabbatar a wata sanarwa.

Sanarwar ta ce, “Sakamakon raunin da ya samu yayin wasa da Olympiacos, an yi wa Romelu Lukaku gwaje-gwaje a asibitin Pineta Grande Hospital, wanda ya bayyana babban rauni a ƙashin cinyarsa ta hagu. Ɗan wasan tuni ya fara samun kulawa kuma zai samu shawar likita kan tiyata.”

An yi wa ɗan wasan ɗan asalin Belgium gwajin likita a asibitin Pineta Grande Hospital, kuma rahotanni sun nuna ya samu babban rauni a ƙashin cinyarsa.

Lukaku dai yana da babban tasiri a ƙungiyar Napoli a baya-bayan nan ƙarƙashin koci Antonio Conte, wanda a baya sun yi aiki tare a Inter.