Adadin mutanen da suka mutu sakamakon hatsarin kwale-kwale a Jihar Bayelsa da ke kudancin Nijeriya ya ƙaru zuwa 29, yayin da ake ci gaba da aikin ceto da gano gawarwakin sauran waɗanda suka mutu.
Hatsarin ya auku ne a ranar Juma’a, 20 ga Nuwamba, 2026, kusa da garin Oweikorogha da ke Ƙaramar Hukumar Southern Ijaw, lokacin da wani kwale-kwale mai ɗauke da fasinjoji, wanda ya taso daga garin Ayama zuwa Ukubie domin halartar wani taron jana’iza, ya kife.
Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, ne ya tabbatar da ƙarin adadin waɗanda suka mutu a ranar Lahadi a Yenegoa, yayin ziyarar da mataimakin shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya kai jihar.
Diri ya ce ba a kai ga tantance ainihin adadin waɗanda suka mutu ba, saboda har yanzu ba a gano kwale-kwalen da ya kife ba. Ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar wasu fasinjoji na maƙale a cikinsa.
Gwamnan ya ce binciken farko ya nuna cewa, da an bi ƙa’idojin tsaron ruwa, da akwai yiwuwar ƙauce wa hatsarin.
A cewarsa, rahotannin farko sun nuna cewa kwale-kwalen ba shi da ingancin da zai iya jigilar fasinjoji, haka kuma wurin da aka loda fasinjojin ba ya cikin wuraren da aka amince da su domin hawa jiragen ruwa.
Gwamnatin jihar na haɗa kai da hukumomin gwamnatin tarayya da jami’an tsaro,da kuma masu sa kai daga al’ummomin yankin domin gudanar da aikin ceto da gano wadanda suka mutu.
Diri ya kuma ce gwamnatin jihar ta dauki nauyin kuɗaɗen jinya da abincin wadanda suka tsira daga hatsarin da ke samun kulawa a asibitoci daban-daban a Bayelsa.
Tinubu ya yi alƙawarin ba da N250M ga iyalan wadanda hatsarin ya shafa
A ɓangare guda kuma, shugaban Nijeriya, Bola Tinubu, ya amince da bayar da tallafin naira miliyan 250 ga iyalan waɗanda hatsarin ya shafa.
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Tinubu ne ya sanar da tallafin a ranar Lahadi yayin ziyarar ta’aziyya da ya kai Bayelsa, inda ya isar da saƙon ta’aziyyar gwamnatin tarayya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.
Haka kuma Shettima ya ce Tinubu ya umarci hukumomin gwamnatin tarayya da su haɗa kai da gwamnatin jihar wajen tallafa wa iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma ƙarfafa ayyukan kai ɗaukin gaggawa.
Kazalika ya bayyana cewa shugaba Tinubu ya umarci Hukumar Kula da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da ta samar da tallafi ga wadanda hatsarin ya shafa.
Haka kuma, shugaban ya umarci ma’aikatar kula da harkokin tattalin arzikin ruwa da ta tabbatar da an aiwatar da dokokin kiyaye lafiyar fasinjoji a hanyoyin ruwa na cikin gida.
An kuma umarci Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC) da ta sayo kwale-kwale domin inganta harkokin sufuri a al’ummomin da ke zaune a yankunan da ruwa ya mamaye.
A yayin ziyarar, mataimakin shugaban ƙasar ya gana da waɗanda suka tsira daga hatsarin da ke karɓar magani a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Kiwon Lafiya ta Bayelsa, tare da jajantawa iyalan waɗanda suka rasa ‘yan’uwansu.
Ya bayyana lamarin a matsayin babban bala’i da ya shafi ƙasa baki ɗaya, yana mai jaddada cewa mutanen da ke amfani da hanyoyin ruwa wajen zirga-zirga sun cancanci samun irin kariyar tsaro da ake bai wa masu amfani da hanyoyin mota da jiragen sama.
Tuni dai gwamnatin jihar Bayelsa ta soma bincike kan musabbabin hatsarin, inda ake sa ran sakamakon binciken zai taimaka wajen ɗaukar matakan hana sake faruwar irin wannan lamari a gaba.
Wannan mummunan hatsari ya sake jawo hankalin jama’a kan batun tsaron fasinjoji a hanyoyin ruwa na Nijeriya, musamman a yankunan da kwale-kwale ke zama sufurin zirga-zirga.

















