Rahotanni sun nuna cewa jirgin alfarma na shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa Cristiano Ronaldo ya bar birnin Riyadh na Saudiyya zuwa Madrid a Spain yayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke ƙara tsananta. Ana zargin cewa an dauki matakin ne yayin da ake fuskantar hare-haren Iran a yankin, wanda ya jawo fargaba a tsakanin mazauna ƙasashen waje.
Ronaldo, wanda ke buga wa ƙungiyar Al Nassr wasa a Riyadh, yana zaune a birnin tare da abokiyar zamansa Georgina Rodríguez da ‘ya’yansu biyar. Rahotanni sun ce jirginsa mai zaman kansa ya tashi daga Riyadh da daddare bayan rikicin ya kara kamari, musamman bayan harin da aka kai kan ofishin jakadancin Amurka a birnin.
Bayanan da shafin Flightradar24 ya wallafa sun nuna cewa jirgin samfurin Bombardier Global Express ya yi kusan awanni bakwai a sama kafin ya sauka a Madrid. Jirgin mai darajar kusan dala miliyan 81 na iya ɗaukar mutum 15, kuma an ce ya tashi daga Riyadh da misalin ƙarfe 8 na dare kafin ya isa Spain da ƙarfe 1 na dare.
Rikicin da ya barke bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran ya sa mutane da dama daga ƙasashen waje ke barin yankin Gabas ta Tsakiya. A lokaci guda kuma, an dage wasu wasannin gasar Zakarun Asiya, abin da ya sa Ronaldo ke cikin hutun wucin gadi daga buga ƙwallo.














