Afirka Afcon 2025 Wasanni

Sarkin Morocco Ya Kira Zaman Lafiya Bayan Rikicin Wasan AFCON Tsakanin Morocco da Senegal

Sarkin Morocco ya ce duk da rikicin da ya faru a wasan karshe na AFCON, zumuncin Afirka zai yi nasara, yayin da CAF da FIFA ke shirin ɗaukar mataki kan abubuwan da suka faru.

Newstimehub

Newstimehub

23 Jan, 2026

0d30d61ae924c14fe7d7602fa97e71f45f4fc3f95eb76fcbb913551edc32f980

Sarkin Morocco, Mohammed VI, ya bayyana cewa zumuncin Afirka zai yi rinjaye duk da “munanan abubuwan” da suka faru a ƙarshen wasan karshe na gasar AFCON tsakanin Morocco da Senegal. Sarkin ya jaddada cewa rikicin da ya barke a mintuna na ƙarshe ba zai lalata kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin al’ummomin Afirka ba.

Wasan ya rikice ne bayan alƙalin wasa ya bai wa Senegal bugun fenariti ta hanyar VAR, lamarin da ya sa ‘yan wasan Senegal suka fice daga fili domin nuna adawa, kafin daga bisani su dawo suka doke Morocco da ci 1–0 bayan ƙarin lokaci. Bayan hukuncin, magoya bayan Senegal sun yi artabu da jami’an tsaro na Morocco yayin da suka yi yunƙurin shiga filin wasa.

A wata sanarwa daga fadar sarauta, Sarkin ya bayyana abubuwan da suka faru a matsayin “abin takaici da abin Allah wadai”, amma ya ce da zarar zafin zuciya ya lafa, zumuncin Afirka zai sake bayyana.

“Babu abin da zai iya lalata ƙawancen da al’ummomin Afirka suka gina tsawon ƙarni, ko haɗin gwiwar da ke ƙara ƙarfafa hulɗa a nahiyar,” in ji Sarkin.

Ya kuma ce gasar ta nuna ci gaban Morocco tare da zama nasara ga Afirka baki ɗaya.

Hukumar CAF ta ce za ta ɗauki matakin da ya dace bayan bincike kan abubuwan da suka faru, yayin da shugaban FIFA, Gianni Infantino, ya yi Allah wadai da halayen wasu ‘yan wasa da jami’an horo na Senegal.

Majiyar Labari: TRT AFRIKA