Afcon 2025 Najeriya Wasanni

Yadda Super Eagles ta doke Taifa Stars a gasar AFCON 2025

Super Eagles ta Nijeriya ta doke Taifa Stars ta Tanzania da ci 2–1 a wasan Rukunin C na AFCON 2025, bayan ƙwallayen da Semi Ajayi da Ademola Lookman suka ci.

Newstimehub

Newstimehub

24 Dec, 2025

e73e3653677be114ed962808b5893e29287a03e8076f0a8584b7d6aac21cc4b3 e1766604703826

Tawagar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya, Super Eagles, ta samu nasara kan tawagar Tanzania, Taifa Stars, da ci 2–1 a wasan Rukunin C na gasar AFCON 2025 da ake bugawa a ƙasar Maroko.

Tun da fari, a minti na 36 ne ɗan wasan Super Eagles, Semi Ajayi, ya fara zura ƙwallo a ragar Tanzania, lamarin da ya bai wa Nijeriya jagoranci kafin a tafi hutun zagayen farko.

Bayan an dawo daga hutun zagaye na biyu, tawagar Tanzania ta farke ƙwallo a mintuna na farko ta hannun Charles M’Mombwa, wanda ya maida wasan 1–1.

Sai dai ba da jimawa ba, ƙasa da mintuna biyu bayan farkewar ƙwallon Tanzania, ɗan wasan Nijeriya Ademola Lookman ya sake zura ƙwallo ta biyu, ya dawo da Nijeriya kan gaba.

An kammala wasan da Nijeriya na da ƙwallaye biyu, yayin da Tanzania ke da ƙwallo ɗaya kacal.

Super Eagles ta fi mamaye wasan musamman a zagayen farko, inda Akor Adams da Victor Osimhen suka rika kai hare-hare masu barazana ga ragar Tanzania.

A Rukunin C na gasar AFCON 2025, ƙasashen da ke fafatawa sun haɗa da Nijeriya, Tunisia, Tanzania da Uganda.

Majiyar Labari: Trt Hausa