Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya nemi a yafewa shari’ar cin hanci da rashawa da ake yi masa, yana mai cewa hakan ya fi dacewa da “maslaha ta ƙasa” domin guje wa rikicewar siyasa da rashin amincewa ga gwamnati, duk da cewa ya ci gaba da musanta laifukan da ake zarginsa da su. Netanyahu ya aika buƙatar afuwar ne ga Shugaba Isaac Herzog, wanda shi kaɗai ke da ikon yanke hukunci kan hakan, lamarin da ya tayar da muhawara a ƙasar, inda masu adawa suka zarge shi da ƙoƙarin tserewa hukunci ba tare da ya amince da laifi ko ya daina siyasa ba; amma abokan siyasar sa sun goyi bayan buƙatar suna ganin tana da muhimmanci ga tsaron ƙasa.
Masana suna gargaɗi cewa, bayar da afuwa kafin hukunci na iya rage darajar tsarin shari’a. Yayin da shari’ar Netanyahu ta farko a tarihin Isra’ila da ta shafi shugaban gwamnati mai ci ke ci gaba a matakai uku na tuhuma da suka haɗa da cin hanci, zamba da karya amana.
Netanyahu Ya Nemi Afuwa a Shari’ar Zargin Cin Hanci da Rashawa
Netanyahu na neman afuwa domin kauce wa rikicewar siyasa, amma adawa na ganin hakan yunƙuri ne na guje wa hukunci ba tare da ya ɗauki alhakin abin da ake zarginsa da shi ba.














