Mutane 38 da aka yi garkuwa da su a cocin Eruku cikin ƙaramar hukumar Ekiti ranar 18 ga Nuwamba 2025 — harin da ya yi sanadin mutuwar mutane uku da jikkatar wani, sun dawo gida lafiya bayan kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane. A wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Ƙaramar Hukumar Ekiti, Dada Sunday, ya fitar a daren Talata, ya ce Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ne ya mika mutanen da aka ceto ga Shugaban Ƙaramar Hukumar Ekiti, Honorabul Awelewa Olawale Gabriel, a Ilorin.
Awelewa ya gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Gwamna AbdulRazaq da hukumomin tsaro bisa gaggawa da ƙoƙarin da suka yi wajen kubutar da mutanen. Ya bayyana cewa haɗin gwiwar jami’an tsaro da gwamnati ya taka rawar gani wajen ceto cikin kankanin lokaci tare da ba waɗanda aka ceto kulawar da ta dace. Sanarwar ta ƙara da cewa tawagar ta isa Eruku da misalin ƙarfe 6:30 na yamma, inda iyalai da mazauna yankin suka tarbe su cikin farinciki da murna. Shugaban ƙaramar hukumar ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da ɗaukar matakan tsaro sosai domin kare rayuka da dukiyoyi a dukkan gundumomi goma na yankin.














