Hukumar shige da fice da hana fasa-ƙauri ta Amurka (ICE) ta tsare tsohon Ministan Kuɗin Ghana, Ken Ofori-Atta, a Amurka. Lauyoyinsa sun bayyana cewa kamun na da alaƙa ne da matsayin zamansa a ƙasar, ba wai wata shari’ar laifi ta daban ba.
A wata sanarwa da ofishin lauyoyinsa, Minkah-Premo, Osei-Bonsu, Bruce-Cathline and Partners (MPOBB), ya fitar a daren Laraba, sun ce tawagar lauyoyin Amurka na tattaunawa da ICE tare da fata cewa za a warware batun cikin gaggawa.
Sanarwar ta ce Ofori-Atta yana da takardar neman gyara matsayin zama (adjustment of status), wadda ke bai wa mutum damar ci gaba da zama bisa doka bayan karewar izinin zama na baya, abin da dokokin Amurka suka amince da shi. Lauyoyin sun jaddada cewa tsohon ministan mutum ne mai bin doka kuma yana ba da cikakken haɗin kai ga ICE domin a kammala shirin cikin lumana.
A gefe guda, Ken Ofori-Atta na fuskantar tuhume-tuhume 78 tare da wasu mutane bakwai kan kwangilolin da aka bai wa kamfanin Strategic Mobilisation Ghana Limited (SML). Ofishin Mai Gabatar da Ƙara na Musamman (OSP) a Ghana ya shigar da ƙarar a watan Nuwamba 2025, yana zargin amfani da ofisoshin gwamnati wajen almundahanar kuɗaɗe, zargin da Ofori-Atta ke ƙaryatawa. OSP ya kuma sanya sunansa a jerin ‘yan sanda na ƙasa da ƙasa a matsayin wanda ake nema ruwa-a-jallo. Ofori-Atta ya kasance a Amurka tun Janairu 2025 domin dalilan lafiya.














