Babbar Kotun Tarayyar Nijeriya da ke Abuja ta ƙi amincewa da buƙatar neman beli da tsohon Babban Lauyan Tarayya kuma Tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya gabatar, bayan tsare shi da Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC). Mai Shari’a Babangida Hassan, wanda ke jagorantar shari’ar, ya yanke hukuncin a ranar Alhamis cewa tsarewar Malami tana bisa doka kuma an aiwatar da ita ne bisa sahihin umarnin kotu. Alkalin ya bayyana cewa hukumar EFCC ba ta karya doka ba wajen tsare tsohon ministan, domin tana bin umarnin da wata kotu mai hurumi ta bayar.
Malami, wanda Babban Lauya ne na Nijeriya (SAN), ya shigar da ƙarar ne ta hannun lauyansa, Sulaiman Hassan, inda ya nemi kotu ta saki shi bisa beli. Ya yi hujjar cewa ci gaba da tsare shi yayin da ake gudanar da bincike ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasa kuma yana take masa ‘yancin walwala. Sai dai hukumar EFCC ta bijire wa wannan buƙata, tana mai cewa tsare Malami yana da sahalewar doka. Lauyan EFCC, J.S. Okutepa, ya shaida wa kotu cewa umarnin tsarewar ya fito ne daga Mai Shari’a S.C. Oriji na wata kotu a Abuja, kuma an bi tanade-tanaden dokar shari’ar manyan laifuka ta ACJA.
A hukuncinsa, Mai Shari’a Hassan ya goyi bayan hujjar EFCC, yana mai jaddada cewa dokar ƙasa da ACJA sun ba da damar tsare mutum bisa sahihin umarnin kotu. Ya kuma bayyana cewa buƙatar da Malami ya gabatar tana da tangarda ta fuskar tsarin shari’a, domin tana neman kotun ta sake duba ko ta soke umarnin wata kotu mai matsayi ɗaya. Alkalin ya ƙara da cewa amincewa da irin wannan buƙata zai sa kotun ta wuce iyakar ikonta, domin hakan zai zama kamar ta zama kotun ɗaukaka ƙara kan hukuncin wata kotu mai matsayi ɗaya.














