Dakta Dominic Akurutinga Ayine, wanda babban Lauyan Ghana kuma Ministan Shari’a na ƙasar, ya miƙa buƙata a hukumance ga Ma’aikatar Shari’a ta Amurka domin a tasa ƙeyar tsohon Ministan Kuɗi na Ghana, Mista Ken Ofori-Atta, da kuma babban mataimakinsa, Mista Ernest Darko Akore, domin su dawo Ghana su fuskanci tuhuma. Da yake magana a taron manema labarai na bayanin ayyukan gwamnati a birnin Accra, Dakta Ayine ya bayyana cewa Ofishin Mai Gabatar da Ƙara na Musamman ya gudanar da bincike kan zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa tsohon Ministan Kuɗin da wasu abokan aikinsa. Ya ce sakamakon binciken ya kai ga shigar da ƙara a Babbar Kotun Shari’a a kansu.
A cewarsa, a ranar 19 ga watan Nuwamba, ofishinsa ya karɓi buƙata a hukumance daga Ofishin Mai Gabatar da Ƙara na Musamman, wadda ke neman a fara matakan tasa ƙeyar Ken Ofori-Atta da Ernest Darko Akore daga Amurka, inda ake zargin suna zaune. Dakta Ayine ya bayyana cewa bayan yin nazari na farko kan buƙatar, Sashen Haɗin Kai na Ƙasa da Ƙasa na ofishinsa ya gano cewa akwai wasu sassa na takardun tasa ƙeyar da ke buƙatar ƙarin bayani da kuma gyare-gyare, domin su cika sharuddan doka da ƙa’idojin tsari da ake buƙata a irin wannan lamari.
Ya ce ofishinsa ya sanar da Ofishin Mai Gabatar da Ƙara na Musamman game da waɗannan buƙatu ta wata wasika mai kwanan wata 25 ga Nuwamba, inda suka nemi ƙarin takardu da bayanai domin cike guraben da aka lura da su. Babban Lauyan ya ƙara da cewa a ranar 9 ga Disamba, Ofishin Mai Gabatar da Ƙara na Musamman ya turo ƙarin takardun da aka nema, tare da gyara wasu kurakurai da aka nuna musu. Wannan ya ba da damar kammala buƙatar tasa ƙeyar yadda doka ta tanada.
Daga bisani, a ranar 10 ga Disamba, ofishin Babban Lauyan Ƙasa ya miƙa cikakkiyar buƙatar tasa ƙeyar ga Ministan Harkokin Waje na Ghana, domin a isar da ita ga hukumomin da suka dace a Amurka, musamman Ma’aikatar Shari’a ta Amurka. “A wannan mataki, al’amari ya koma hannun hukumomin Amurka, musamman na shari’a, su tantance ko akwai isasshen dalili da zai sa a tasa ƙeyar waɗannan mutane biyu zuwa Ghana domin su fuskanci shari’a,” in ji Dakta Ayine.
Gwamnatin Ghana ta miƙa buƙata ga Amurka domin tasa ƙeyar tsohon Ministan Kuɗi Ken Ofori-Atta da mataimakinsa bisa zargin cin hanci. Yanzu dai hukuncin ko za a miƙo su ya rage a hannun hukumomin shari’a na Amurka.














