Amurka ta sanar da rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta shekaru biyar da Nijeriya, domin inganta tsarin kiwon lafiya a ƙasar, duk da zarge-zargen da Shugaba Donald Trump ya yi a baya kan tsangwamar Kiristoci. A ƙarƙashin yarjejeniyar, Amurka za ta bayar da kusan dala biliyan 2.1 don yaƙi da cututtuka kamar HIV, tarin fuka, zazzaɓin cizon sauro da polio, tare da kare lafiyar mata masu juna biyu da yara.
A nata ɓangaren, Nijeriya ta yi alƙawarin zuba kusan dala biliyan 3 a cikin shekaru biyar masu zuwa, yayin da yarjejeniyar ke kuma bai wa cibiyoyin kiwon lafiya masu alaƙa da Kiristoci muhimmanci. Wannan mataki ya zo ne bayan Amurka ta sanya Nijeriya cikin jerin ƙasashen da take sanya wa ido kan batun ’yancin addini, duk da cewa hukumomin Nijeriya sun musanta zargin nuna wariya ga kowanne addini.
Yarjejeniyar ta biyo bayan sauye-sauyen da gwamnatin Nijeriya ta ce ta yi domin rage tashin hankali, a ƙasar da ke fama da rikice-rikicen ƙabilanci, addini da ta’addanci, waɗanda suka janyo asarar rayuka da gudun hijira ga miliyoyin mutane.














