Dubban fararen hula a Sudan sun tsinci kansu cikin halin gudun hijira bayan mayaƙan Rundunar RSF sun ƙwace iko da birnin Al Fasher da wasu yankunan da ke kewaye da shi a Jihar Darfur ta Arewa. Rahotanni sun nuna cewa tsananin rashin tsaro ya tilasta wa mutane barin gidajensu domin tsira da rayukansu.
Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (IOM) ta ce aƙalla mutane 107,294 daga iyalai 24,221 ne suka rasa matsugunansu tsakanin 26 ga Oktoba zuwa 8 ga Disamba, lokacin da yanayin tsaro ya ƙara tabarbarewa bayan RSF ta karɓe iko da yankin.
A cewar hukumar, kusan kashi 72% na waɗanda suka tsere sun rage ne a cikin Arewacin Darfur, yayin da kashi 19% suka koma wasu jihohi kamar Tsakiyar Darfur, Jihar Arewa da White Nile. IOM ta ƙara da cewa yawancin mutanen sun riga sun taɓa rasa matsugunansu a baya, musamman daga sansanonin ‘yan gudun hijira irin su Zamzam da Abu Shouk.
Hukumar ta yi gargaɗin cewa ci gaba da rashin tsaro da takunkumin zirga-zirga na iya ƙara tsananta halin da jama’a ke ciki. Rikicin da ke tsakanin sojojin Sudan da RSF tun daga Afrilun 2023 ya kashe dubban mutane tare da tilasta wa miliyoyin fararen hula barin gidajensu.














