Jami’an Hukumar Kwastam ta Nijeriya (NCS) sun kama kwantena 20 da aka karkatar da su ɗauke da kayayyaki masu darajar kuɗi har naira miliyan 769.5 a jihohin Kano da Jigawa, biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka tattara. Wannan kamen na daga cikin ƙoƙarin hukumar na dakile fasa-ƙwauri da kare tattalin arzikin ƙasa.
Shugaban Hukumar Kwastam, Bashir Adeniyi, ya ce kamen ya samo asali ne daga ayyukan leƙen asiri da aka gudanar a rubu’i na biyu da na huɗu na shekarar 2025, da nufin tarwatsa wata ƙungiya da ke karkatar da kwantena a manyan titunan ƙasar. A cewarsa, karkatar da kwantena babban laifi ne da ke janyo asarar kuɗaɗen shiga ga gwamnati, barazana ga tsaron ƙasa, da lalata martabar Nijeriya a kasuwancin duniya. Ya tabbatar da cewa hukumar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen hukunta duk masu aikata irin wannan laifi.
Kayayyakin da aka kama sun haɗa da tayal da aka yi amfani da su ba bisa ƙa’ida ba, man dizal, kayan sawa, yadudduka, leshi, kayan asibiti, da ruwan Zamzam, inda wasu daga cikinsu ke cikin jerin abubuwan da doka ta haramta shigo da su ƙasar.
Hukumar ta kuma tabbatar da yanke wa wani Abdulrahman Sani Adam hukuncin daurin shekaru uku ko biyan tarar naira miliyan uku, tare da sanar da cewa ana shirin kammala aikin kafa na’urorin bin diddigin kwantena na lantarki domin ƙara sa ido kan jigilar kaya.














