Afirka Ajanda

DRC ta sake buɗe kasuwar fitar da Cobalt bayan dakatarwa ta watanni 10

DRC ta sake fara fitar da ma’adinin cobalt bayan dakatarwa ta watanni 10, lamarin da ya haifar da ƙaruwa sosai a farashinsa a kasuwannin duniya.

Newstimehub

Newstimehub

23 Dec, 2025

download 2 e1766517595513

Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo ta dawo fitar da ma’adinin Cobalt, wanda ake amfani da shi wajen ƙera kayan lantarki, bayan ta dakatar da fitar da shi tsawon watanni 10 domin daidaita farashinsa da na kasuwannin duniya.

Ministan kudin kasar Doudou Fwamba ya ce matakin da aka gabatar ya yi amfani, kuma za a fitar da sabon tsarin yadda fitar da ma’adinin za ta kasance.

Ya ce farashin cobalt ya karu da kusan kashi 50 cikin 100, inda a baya ake saida tan 1 kan farashin dala dubu 22, yanzu kuma ya kusan dala dubu 50.

Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo dai na sahun gaba a duniya wajen samar da ma’adinun na Cobalt da ake amfani da shi wajen yin batiran wayar salula da kayan laturoni da mota mai aiki da lantarki.

Majiyar Labari: BBC Hausa