Harin bam da ya afku a wani masallaci a kasuwar Gamboru, birnin Maiduguri na jihar Borno, ya sake tayar da hankulan jama’a bayan da aka tabbatar da mutuwar Musulmi biyar tare da jikkatar wasu da dama, lamarin da ya sa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin ƙara tsaurara ayyukan tsaro a yankin.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya yi kakkausar suka kan harin, yana mai bayyana shi a matsayin mummunan ta’addanci kan fararen hula da zaman lafiyar Najeriya. Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:10 na yammacin Laraba a unguwar Gamboru, kusa da yankin Kwastam, yayin da Musulmi ke tsaka da sallar Magariba, sa’o’i kaɗan kafin bikin Kirsimeti.

Wannan bayani ya fito ne ta cikin wata sanarwa da Stanley Nkwocha, Mataimakin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai, ya fitar a ranar Alhamis.
A cewar sanarwar, Shugaba Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da su ƙara tura rundunonin musamman zuwa Maiduguri da sauran sassan jihar Borno, domin gano tare da kama waɗanda ke da hannu a harin bam ɗin da ake zargin ‘yan Boko Haram ne suka kai.
Shettima ya jaddada cewa gwamnatin tarayya ba za ta lamunci duk wani yunƙuri na lalata tsaro ko tayar da zaune tsaye a Najeriya ba, yana mai tabbatar da cewa za a hukunta masu laifi bisa doka.
Mataimakin shugaban ƙasar ya miƙa ta’aziyya ga gwamnatin jihar Borno, al’ummar Maiduguri da iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, yana mai ƙarfafa gwiwar jama’a cewa ƙudirin gwamnatin Tinubu na yakar ta’addanci da tabbatar da tsaro bai sauya ba.
Ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya na aiki tare da hukumomin jihohi da na ƙananan hukumomi domin kare rayuka, dukiyoyi da muhimman gine-gine a Arewa maso Gabas da sauran sassan ƙasar.














