Hafsoshin soji da suka yi murabus da abokan marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar (murabus) sun yi kira da a yi cikakken garambawul ga tsarin tsaron Nijeriya biyo bayan mutuwar janar ɗin mai ritaya bayan ‘yanbindiga sun yi garkuwa da shi a Jihar Katsina.
Sun yi wannan kiran ne ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai a Kaduna wanda Birgediya Janar Isma’ila Abdullahi (murabus) ya jagoranta, inda ya yi jawabi a madadin abokan aiki da abokan marigayin.
Sauran manyan waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Birgediya Janar Abubakar Abdulqadir (murabus) da Birgediya Janar M.I. Tsiga (murabus) da Air Commodore Yusuf Anas (murabus) da Ambassada Ibrahim Usman Gafai da kuma Ambassada Ahmed Muhammad Musawa, kamar yadda kafar Channels ta ruwaito
Abdullahi ya bayyana rasuwar Janar Abubakar a matsayin wani bala’i da ke tuna wa mutane ƙaruwar rashin tsaro a faɗin ƙasar, suna masu cewa hafsan da ya yi murabus ya rasu ne bayan ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shi a yankin Matazu a jihar Katsina.
“Abokin aikinmu, abokinmu da kuma ɗan’uwanmu, Manjo Janar Rabe Abubakar (murabus), ya rasu bayan mugayen ‘yanbindiga sun yi garkuwa da shi. Rasuwarsa bagatantan ya tayar mana hankali kuma ya ɓata mana rai,” in ji shi .
Yayin da yake cewa ya san da ƙoƙarin da gwamnatin tarayya da gwammnatin jihar Katsina suka yi wajen ceto matar marigayin, Hajiya Amina Rabe Abubakar, Abdullahi ya ce lamarin ya nuna buƙatar gaggawa ta ɗaukar matakai masu ƙarfi wajen yaƙar fashin daji da garkuwa da mutane da ta’addanci.
Ya ce kashe janar ɗin mai murabus ya nuna ƙalubalen tsaro mai faɗi da ke fuskantar Nijeriya.
“Mutuwar Janar Rabe Abubakar ba wai kanun labarai ba ne kawai ba. Ya nuna matsalolin tsarin tsaron ƙasar domin tabbatar da tsaron ‘yanƙasa. Garkuwa da mutane da fashin daji da ta’addanci sun zama abu mai zafi ga da yawa daga cikin ‘yan Nijeriya,” a cewarsa.
Hafsan mai ritaya ya nuna damuwa kan yaɗuwar rashin tsaro a fadin sassan ƙasar kuma ya yi gargaɗi game da siyasantar da lamarin ko kuma yi masa kallon lamari na ƙabailanci ko kuma na ɓangaranci.
Sun jaddada cewa ta’addanci da garkuwa da mutane da fashin daji matsaloli ne da ke buƙatar martani na haɗin kai daga dukkan masu ruwa da tsaki.
“Dole mu ƙi yarda da siyasantar da rashin tsaro. Wannan matsala ce ta Nijeriya wadda ke buƙatar mafita ta haɗin gwiwa ta ƙasa,” kamar yadda Abdullahi ya bayyana.
Tsaffin hafsoshin sojojin sun nemi a ƙarfafa hukumomin tsaro da kuma ingnata haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da kuma ƙarin zuba jari wajen tattara bayanan sirri da kuma kare kan iyakoki domin daƙile kwararowar makamai ba bisa ƙa’ida ba.
Sun kuma yi maraba da haɗin gwiwa da ƙasashen ƙetare wajen yaƙar ta’addanci , amma sun ce ainihin nauyin kare ƙasar ya rataye ne a wuyar hukumomin Nijeriya.
“Babu wata ƙasa ta ƙetare da za ta iya tsare mana Nijeriya. Haɗin gwiwa da ƙasashen waje yana da muhimmanci, nauyin kare ‘yan Nijeriya yana rataye ne a kan hukumominmu da shugabanni,” a cewarsu.
Da yake amsa tambayoyi daga ‘yanjarida, Abdullahi ya nemi inganta tallafin ga tsarin tsaron na cikin al’ummomi, musamman a yankunan karkara da ‘yanbindiga suke yawan kai wa hari .
Ya ce ya kamata a bai wa ‘yan sa-kai kayayyakin aikin da suka dace da horo domin taimakawa wajen kare al’ummomin da ke fuskantar barazana.
“A lokacin da ‘yanfashi masu manyan makamai suka kai hari kan al’umomi, abu ne da ya saɓa wa hankali a yi tsammanin masu kare al’ummomi su dogara ga kayayyakin aiki na da can.
“Alummomi za su iya tsari da kuma horas da zaɓaɓɓun matasa a ƙarƙashin kulawa na musamman domin tallafa wa ƙoƙarin tsaro na yankunan su,” a cewarsa.
Sai dai kuma, ya yi gargaɗi kan kwararar makamai babu ƙaƙƙautawa yana mai tattabatar da cewa duk wani tsarin kare al’umma dole ya yi aiki bisa ƙa’ida da sa-ido sosai.
Hafsoshin da suka ritaya sun kuma nemi gwamnatin jihar ta kafa rundunonin tsare dazuka da kuma taimaka wa ƙoƙarin ɗaukar jami’ai da cikakken horaswa da jigila da aiki.
“Kafa rundunar tsare dazuka mataki na farko ne kawai. Horaswan da ya dace da kuma kayayyaki suna da muhimmanci idan za su ba da gudumowa mai ma’ana wajen yaƙar rashin tsaro a cikin dazuka,” a cewar Abdullahi.
Game da batun kafa ‘yansandan jihohi, ƙungiyar ta ce tana goyon bayan tsarin, amma ta yi imanin cewa jihohin da ke da ƙarfi na kuɗi da kuma ƙwarewar iya tafiyar da irin wannan hukumar ce ya kamata a bai wa damar kafa irin wannan hukumar.
“Ba ma adawa da rundunar ‘yansanda mallakar jiha. Sai dai kuma, jihohi da ke neman kafa irin wannan tsarin dole su nuna ƙarfin iya ɗaukar ma’aikata da horas da su da kuma ba su kayayyakin aiki kamar yadda ya dace,” a cewarsa.
Hafsoshin da suka yi ritayar sun kuma yi kira ga gwamnatoci a duk mataki su ba da tallafi ga iyalan da garkuwa da mutane da ta’addanci da fashin daji ya shafa, yayin da suke zafafa ƙoƙarin tabbatar da cewa an saki dukkan ‘yan ƙasa da ake garkuwa da su.

















