Shugaban Rasha Vladimir Putin ya aika da wani muhimmin saƙo ga Shugaban Amurka Donald Trump game da yiwuwar yarjejeniyar zaman lafiya a Ukraine, bayan Moscow ta karɓi shawarwari daga Amurka kan kawo ƙarshen yaƙin, in ji fadar Kremlin.
Kakakin Kremlin Dmitry Peskov ya ce mai bai wa Putin shawara kan harkokin waje, Yuri Ushakov, ya tattauna ta wayar tarho da wasu jami’an gwamnatin Trump. Sai dai bai bayyana ainihin lokacin da aka yi tattaunawar ba. A cewarsa, wakilin Putin, Kirill Dmitriev, ya dawo Moscow dauke da takardun shawarwarin zaman lafiyar da ya karɓo daga Amurka bayan wani taro da aka yi a Miami.
Peskov ya bayyana cewa Kremlin na nazarin shawarwarin cikin tsanaki, inda ya ce an amince a ci gaba da tattaunawa tsakanin Rasha da Amurka. Ya ƙi yin tsokaci kan abun da ke cikin takardun, yana mai cewa bayyana bayanai a bainar jama’a na iya kawo cikas ga shawarwarin diflomasiyya.
A wani rahoto da jaridar Kommersant ta Rasha ta wallafa, an ce Putin ya bayyana wa wasu manyan ‘yan kasuwa a ƙasar cewa yana iya amincewa da musayar wasu yankunan da sojojin Rasha ke iko da su a Ukraine, amma yana son cikakken ikon yankin Donbas. Kremlin dai bai tabbatar da wannan bayani dalla-dalla ba, sai dai ya ce batun zaman lafiyar Ukraine an taɓo shi gaba ɗaya a tattaunawar.














